Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-24 16:04:42    
Shiyyar kudu maso gabashin Afirka tana dosawa gaba bisa tsarin tattalin arziki na bai daya

cri
A ran 23 ga wata a birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya, an rufe taro shugabanni na 12 kan kasuwar bai daya ta kudu maso gabashin Afirka, a gun taron an zartas da kudurin kafa kawancen kudin kwastan na kudu maso gabashin Afirka, wannan ya alamta cewa, kungiyar tattalin arziki mafi girma ta shiyya-shiyya ta Afirka ta kara dosawa gaba bisa tsarin tattalin arziki na bai daya. To jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku wani bayani da wakilinmu ya ruwaito mana kan wannan labari.

A gun bikin rufe taron da aka yi a wannan rana, Mr. Mukhisa Kituyi, shugaban majalisar ministocin kasuwar bai daya ta kudu maso gabashin Afirka, kuma ministan ciniki da masana'antu na Kenya ya karanta sanarwar wannan taro. Ya ce, "Taron koli ya nanata alkawarin da ya dauka cewa, za a kafa kawancen kudin kwastan na kudu maso gabashin Afirka a ran 8 ga watan Disamba na shekarar 2008, a lokacin kuwa za a buga harajin kwastan iri daya kan kayayyakin da kasashe mambobi daban-daban na kawance za su shigo da su daga kasashen da ba na kawancen ba, wato za a soke harajin kwastan kan danyun kayayyaki da kayyakin jari, yawan harajin kwastan da za a buga kan kayayyakin da ba a gama ba ya kai kashi 10 bisa 100, harajin kwastan na kayayyakin da aka gama kuma ya kai kashi 25 bisa 100."

Kungiyar tattalin arziki ta kasuwar bai daya ta kudu maso gabashin Afirka ita ce kungiyar tattalin arziki mafi girma ta shiyya- shiyya ta Afirka, wadda ta kafu a watan Disamba na shekarar 1993, yanzu tana da kasashe mambobi 20. A watan Oktoba na shekarar 2000, kungiyar nan ta bude shiyyar yin ciniki ba tare da cikas ba ta farko ta Afirak wato shiyyar yin cinikin bai daya ta kudu maso gabashin Afirka. Yanzu an riga an yi shekaru 7 ke nan da aka kafa wannan shiyyar yin ciniki ba tare da cikas ba, amma har ila yau da akwai kasashe mambobi 13 kawai daga cikin wadannan kasashe mambobi 20 wadanda suka shiga cikin shiyyar yin ciniki ba tare da cikas ba, Mr. Kituyi ya ce, "Taron koli ya gamsu da saurin ci gaba da kuma karuwa mai dorewa da aka samu wajen cinikin da aka yi daga shekarar 2005 zuwa ta 2006 cikin kasuwar bai daya ta kudu maso gabashin Afirka, kuma ya nuna yabo ga kasashe mambobi sabo da suka yarda da cire shingen ciniki ba tare da buga kudin kwastan ba. Taron koli ya sa kaimi ga kasashe mambobi wadanda har yanzu ba su shiga cikin shiyya yin ciniki ba tare da cikas ba da su shiga cikin shiyyar tun kafin watan Disamba na shekarar 2008, wato kafin lokacin kafa kawancen kudin kwastan."

Ko da yake kasashe mambobi daban-daban na kasuwar bai daya ta kudu maso gabashin Afirka sun samu ra'ayi daya daga wasu fannoni a gun wannan taron koli ko kafin wannan taro, amma har ila yau kara saurin ci gaba da kuma kyautata tsarin tattalin arziki na bai daya ya zama aikin farko ne ga wannan kungiya. Game da wannan batu, Mr. Mwai Kibaki, shugaban kasuwar bai daya ta kudu maso gabashin Afirka ta zagaye mai zuwa, kuma shugaban kasar Kenya ya bayyana cewa, "Kasashe mambobin kasuwar bai daya ta kudu maso gabashin Afirka sun riga sun samu babbar nasara wajen sa kaimi ga bunkasa shiyyar nan, buri mafi girma da muke sa wa wannan taron koli shi ne, bisa harsashin nasarorin da aka samu, za a kara kyautata tsarin tattalin arziki na bai daya na shiyya-shiyya. Babban take na wannan taro ya bayyana wannan makasudinmu da kyau, wato shi ne "kara kyautata tsarin tattalin arziki na bai daya na shiyya-shiyya, da yin hidima ga aikin bunkasa tattalin arziki daga fannoni da yawa da samun karin kudi da yawa wajen tattalin arziki." (Umaru)