Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-23 15:38:43    
Aikin kiyaye kayayyakin tarihi na birnin Beijing ya kara kyautata wasannin Olimpic da suka dace da al'adun 'yan Adam

cri

Lokacin yin wasannin Olimpic na shekarar 2008 yana kusan zuwanmu, birnin Beijing yana nan yana kokarin yin ayyukan share fage iri daban daban. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, birnin Beijing ya yi ta kara karfinsa na aiwatar da ayyukan kiyaye kayayyakin tarihi wadanda suke zama daya daga cikin ayyukan raya wasannin Olimpic da suka dace da al'adun 'yan adam. Kwanan baya, an nemi sassa 18 na kiyaye kayayyakin tarihi da su kyautata sharudan kiyaye kayayyakin tarihi. Shugaban hukumar kiyaye kayayyakin tarihi na birnin Beijing Mr Kong Fanzhi ya bayyana cewa, aikin kiyaye kayayyakin tarihi na birnin Beijing kamata ya yi ya kafa muhalli mai kyau ga yin wasannin Olimpic.

An kafa hedkwatar kasa a birnin Beijing cikin shekaru da yawansu ya kai 850, kayayyakin tarihi na zamani aru aru suna kasancewa a wuraren birnin Beijing a ko'ina, yawan hukumomin kiyaye kayayyakin tarihi ya kai dubu 2 ko fiye bisa matakai daban daban. Dayake wadannan kayayyakin tarihi suna da shekaru da yawa sosai, har ma yawancinsu su ne gine-ginen gargajiya da aka gina su ta hanyar yin amfani da kasa da katako, saboda haka an riga an lalatasu da yawa, ko ma an gina su ne ba tare da shirya kayayyakin kashe gobara da na kawar da hadarin cida da dai sauransu, saboda haka a shekarar 2000, birnin Beijing ya soma ayyukan gyara kayayyakin tarihi, kuma gwamnatin birnin ta ware kudade da yawansu ya kai kudin Sin Yuan miliyan 330 don gyara kayayyakin tarihi cikin shekaru uku, sa'anan kuma sauran yankuna da gundumomi su ma sun ware kudadensu wajen ayyukan, har ma yawan kudadden da aka ware ya riga ya kai kudin Sin Yuan miliyan dubu 5, wannan dai ba a taba ganinsu ba a tarihin kasar Sin.

A farkon shekarar da muke ciki, hukumar kiyaye kayayyakin tarihi na birnin Beijing ya yi bincike sosai kan wasu matsalolin da ke kasancewa kuma watakila za su kawo haddurdura, sa'anan kuma ya mayar da sassa 18 da su zama sassan da aka sa ido sosai a kansu. Mataimakiyar shugaba ta hukumar kiyaye kayayyakin tarihi ta birnin Beijing malama Yu Ping ta bayyana cewa, yanzu, mun riga mun bayar da takardu ga wadannan sassa 18 da su yi gyare-gyare cikin kayadadden lokaci, kuma mun mayar da wadannan sassa bisa matsayin ayyukan da muka sa ido sosai a kansu a shekarar 2007, sa'anan kuma za mu taimake su don tsara shirin warware matsalolin .

Shugaban hukumar kiyaye kayayyakin tarihi Mr Kong Fanzhi ya kuma bayyana cewa, aikin daidaita cikas da aka samu wajen kiyaye kayayyakin tarihi yana da ma'ana mai muhimmanci a halin yanzu, wadannan matsalolin da aka samu a kan batun kiyaye kayayyakin tarihi ba su dace da muhallin da ake kasancewa a hedkwatar kasar Sin da halin da ake ciki na shirya wasannin Olimpic ba, dole ne a dauki matakai da kuma daidaita wadannan matsaloli a daidai lokaci , gine-ginen tarihi na yin wasannin Olimpic su ne wani kashi mai muhimmanci da ke cikin muhallin al'adu na hedkwatar kasar Sin , ya kamata batun kiyaye su zai kafa muhallin al'adu ga wasannin Olimpic .

Birnin Beijing ya sami sakamako sosai wajen kiyaye kayayyakin tarihi na al'adu. Wato an riga an gyara babbar kofar Yongdingmen ta tsohon birnin Beijing, sa'anan kuma kayayyakin tarihi na duniya da suka hada da tsohuwar fadar sarakuna wato Gugong da tsohon wurin da mutanen Beijing na zamani aru-aru suke zama a Zhoukoudian na birnin Beijing da Tiantan , wato wurin da sarakuna suka yi bikin girmama sararin samaniya na birnin Beijing da babbar ganuwar kasar Sin da dai sauransu.Mataimakiyar shugabar hukumar kiyaye kayayyakin tarihi na al'adu ta birnin Beijing malama Yu Ping ta bayyana cewa, bisa albarkacin samun bunkasuwar tattalin arziki, mutane suna da karfi kuma kasa tana da dukiyoyi da kudade wajen kare kayayyakin tarihi na al'adu.(Halima)