Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-23 15:34:47    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(17/05-23/05)

cri

Da farko akwai labaru 2 game da taron wasannin Olympic na Beijing na shekara ta 2008. An bude taron dandalin duniya kan taron wasannin Olympic na Beijing da aikin yawon shakatawa a birnin Qingdao na kasar Sin a ran 17 ga wata. A cikin wasikar taya murna, mataimakiyar firayim minista madam Wu Yi ta kasar Sin ta bayyana cewa, taron wasannin Olympic na Beijing na shekara ta 2008 zai kawo wa kasar Sin kyakkyawar dama a fannin raya sha'anin yawon shakatawa. Ta kara da cewa, wasannin Olympic da aikin yawon shakatawa suna taimakawa juna yadda ya kamata, suna sa kaimi ga juna. Kasar Sin na mallakar albarkatun yawon shakatawa masu dimbin yawa. A shekarun baya da suka wuce, ta sami saurin bunkasuwar aikin yawon shakatawa, ta kyautata ayyukan da suka shafi sha'anin yawon shakatawa a kwana a tashi, ta kuma daga matsayin ba da hidima a bayyane, sa'an nan kuma ta yi ta zurfafa mu'amala da hadin gwiwa a tsakaninta da kasashen duniya ta fuskar yawon shakatawa. Tabbas ne taron wasannin Olympic da za a yi a Beijing a shekara mai zuwa zai samar wa kasar Sin babban karfi wajen raya aikin yawon shakatawa.

A wata sabuwa kuma, a gun taron manema labaru da aka yi kan wasannin Olympic da bunkasuwar Beijing a ran 16 ga wata da yamma, mataimakin darektan kwamitin yin gyare-gyare da raya birnin Beijing Lu Yingchuan ya ba da rahoto, inda ya nuna cewa, shekara daya da ta gabata, 'yan birnin Beijing sun raya zaman rayuwarsu mai matsakacin karfi daga dukkan fannoni. Kudin shiga da suka samu ya yi ta karuwa. An kyautata zaman rayuwar fararen hula, sa'an nan kuma, 'yan birnin sun kyautata zamansu na al'ada sannu a hankali.

A 'yan kwanaki da suka wuce, a birnin Zurich na kasar Switzerland, shugaba Blatt na hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya wato FIFA ya sanar da cewa, mai yiwuwa ne za a kara yawan kungiyoyin wasan kwallon kafa na mata daga 16 zuwa 24, wadanda za su shiga gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta mata ta shekara ta 2011. An ce, yanzu kasashe 6 wato Canada da Faransa da Jamus da Switzerland da Australia da kuma Peru sun gabatar da rokon neman samun damar shirya wannan muhimmiyar gasa. Kungiyar FIFA za ta sanar da kasar da za ta sami wannan kyakkyawar dama a watan Disamba na wannan shekara.(Tasallah)