Bisa labarin da muka samu daga kamfanin dillancin labaru na Xinhua, an ce, a ran 22 ga wata Liu Guijin wakilin musamman mai kula da batun Darfur na gwamnatin Sin ya ziyarci shiyyar Darfur dake yammancin kasar Sudan don nazarin halin da ake ciki a Darfur.
Mr.Liu Guijin ya ziyarci El Fashir hedkwatar jihar arewancin Darfur da Nyala hedkwatar jihar kudancin Darfur bi da bi, ya yi rangadi a sansanonin 'yan gudun hujira guda 3 dake wurin, kuma ya sa kafa a kan manyan tituna da kasuwoyi na wannan gari don gane ma idonsa, kuma ya yi hira da mazaunan wurin.
Ban da wannan kuma Mr.Liu Guijin ya zanta da jami'an wurin ciki har da gwamnonin jihohin nan 2 da wakilan bangarori daban daban, ya bayar da jawabi cikin majalisar wakilan jiha da taron maraba da fararen hula suka shirya.
Ya jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin tana fatan za a daidaita batun Darfur yadda ya kamata kuma cikin sauri don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a duk fannoni tun da wuri.(Salamatu)
|