Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-22 17:57:56    
Kamata ya yi gwamnatocin kasashen Afirka da jama'arsu su kasance ke kula da harkokin gidansu

cri

Yau Talata a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, Madam Jiang Yu ta bayyana cewa, Sin tana ganin cewa, ya kamata gwamnatocin kasashen Afirka tare kuma da jama'arsu su kasance ke kula da harkokin gidansu.

Madam Jiang Yu ta yi wannan furuci ne a gun taron manema labarai da aka shirya a ran nan. Ta ce, kamata ya yi taimakon da kasashen duniya suka baiwa Afirka ya kasance mai amfani, kuma ya kamata taimakon ya amfana wajen sa kaimi ga kasashen Afirka da su tabbatar da kwanciyar hankalinsu da kuma ci gabansu bisa kokarinsu.

Madam Jiang Yu ta ce, har kullum Sin tana bin manufar diplomasiyya ta zaman kanta, kuma ba ta taba tilasta wa sauran kasashe da su bi tunaninta ko kuma tsarin ci gabanta ba, kullum Sin tana bin tsarin ka'idojin MDD da kuma ka'idojin da ke shafar huldar da ke tsakanin kasa da kasa a yayin da take bunkasa huldar da ke tsakaninta da saurna kasashe. (Lubabatu)