Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-22 15:17:59    
Kallon talibijin kullum zai iya yin illa ga yara wajen cin abinci

cri

A kwanan nan, manazarta na jami'ar Harvard ta kasar Amurka sun gabatar da wani rahoto ga kungiyar kula da zuciya ta kasar, inda suka bayyana cewa, lokacin da yara suke kallon talibijin, su kan yi kalaci sosai. Kuma sannu a hankali za su kirkiri dabi'ar cin abinci maras kyau, wadda za ta haddasa karuwar yawan nauyin jiki.

Manazarta sun gudanar da wani bincike ga yara 1203 da shekarunsu ya kai 3 da haihuwa kan abubuwan da suke yi lokacin da suke kallon talibijin. Daga baya kuma sun gano cewa, kusan dukkan yara su kan sha abinsha ko cin abinci lokacin da suke kallon talibijin. Sabo da wadannan yara sun yi kalaci maras kyau fiye da kima lokacin da suke kallon talibijin, shi ya sa ba safai su kan so cin abinci a lokcin cin abinci yadda ya kamata ba. Sabo da haka kuma yawan 'ya'yan itatuwa da kuma kayayyakin lambu da dai sauran abinci masu gina jiki da yaran da suke son kallon talibijin su kan ci ya yi kadan idan an kwatanta shi da na yaran da ba su son kallon talibiji.

Ban da wannan kuma rahoton ya bayyana cewa, idan tsawon lokacin kallon talibijin ya karu, sai yawan abinci da yara suka ci ya karu, kuma yawan sinadarin calorie da suke samu daga abinci ya karu, a waje daya kuma yawan lokacin motsa jiki ya ragu, sabo da haka yaran da su kan yi kallon talibijin sun fi saukin samun kiba. Bugu da kari kuma manazarta sun bayyana cewa, idan yawan lokacin kallon talibijin ya karu da awa guda, to yawan sinadarin calorie da yara suka samu daga abinci zai karu da 46. A kwana a tashi, wannan zai iya yin illa ga lafiyar jikinsu.

Sabo da haka kungiyar kula da zuciya ta kasar Amurka ta ba da shawarar cewa, ya fi kyau yara su kwashe awa guda ko biyu wajen kallon talibijin a ko wace rana, kuma ya fi kyau kada iyaye su ajiya talibiji a dakin yara.

Mutane masu basira tunaninsu iri daya ne. Bayan da Dr. Aric Sigman, wani kwararren kasar Birtaniya a fannin ilmin tananin dan Adam ya yi nazari, ya gano cewa, kallon talibijin kullum zai iya rage yawan wani irin sinadarin hormone da yara su kan fitar wanda ake kiransa melatonin, ta haka zai iya yin illa gare su wajen tsarin garkuwar jiki da yanayin barci da kuma lokacin girma.

Haka kuma nazarin ya bayyana cewa, idan yawan sinadarin melatonin da ke cikin jikin yara mata ya yi kadan sosai, to za su shiga lokacin balaga tun da wuri. Ban da wannan kuma kwayoyin da ke cikin jikin yara za su fi saukin lalatace har su kamu da sankara.

Sabo da haka, Dr. Sigman ya yi kira ga gwamnatin kasar Birtaniya da ta daukai tsauraran matakai kan tallafa wa yara wajen rage yawan lokacin kallon talibijin, ta yadda za su iya samun lafiyar jiki.(Kande)