Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-22 15:13:54    
Tabkin Nanbeihu na lardin Zhejiang

cri

Tabkin Nanbeihu yana cikin gundumar Haiyan na lardin Zhejian, yana da nisan kilomita misalin 80 a tsakaninsa da birnin Hangzhou, babban birnin Zhejiang a gabas, yana samar wa masu yawon shakatawa kwanciyar hankali, wanda ya sha bamban da na wani shahararren tabki daban wato tabkin Xihu da ke Hangzhou. Wata madatsar ruwa ta raba wannan tabki zuwa kashi 2, wato na kudu da na arewa. Ko da yake karami ne, in an kwatanta da shi da tabkin Xihu, amma a can da tabkin Nanbeihu na da muhimmanci sosai wajen magance ambaliyar ruwa, saboda an hada shi da kogin Qiantangjiang.

Wannan tabki mai fadin murabba'in misalin kadada 122 ya fara jawo hankulan masu yawon shakatawa tun daga zamanin daular Song, wato tsakanin shekara ta 960 zuwa ta 1279, a lokacin can, ya yi suna ne sosai har ma ana kiransa karamin tabkin Xihu. An gina lambuna da gadoji da rumfuna a kewayensa. Saboda ya yi nisa da manyan birane, kuma manyan duwatsu kwarra suna yin garkuwa da shi, shi ya sa mutane ke iya sakin jiki a lokacin da suke yawo a kewayen tabkin Nanbeihu.

An raya tabkin Nanbeihu zuwa wani wurin shakatawa mai fadin murabba'in misalin kilomita 30. A kan gangarar rairayin bakin tabkin, wani dan kasuwa na wurin ya gina wani makeken gida irin na alfarma mai suna Zaiqing a shekara ta 1916. Shugaban siyasa marigayi Kim Koo na kasar Korea ta Kudu, wanda ya ya jagoranci ayyukan neman samun 'yancin kan kasarsa, ya taba yin mafaka a nan. Bayan da ya shirya wani gaggarumin bore don yaki da mahara Japanawa a birnin Shanghai, wannan dan kishin kasa ya koma da baya, ya yi rabin shekara yana zama a cikin wannan makeken gida irin na alfarma. Ko da yake an taba rushe shi, amma a shekara ta 1995, gwamnatin Sin ta sake gina wannan makeken gida irin na alfarma don tunawa da wannan abokinta na kasar Korea ta Kudu, wanda a idon matarsa 'yar kasar Sin, ya iya Sinanci sosai, har ma shi dan birnin Guangdong ne a maimakon dan kasar Korea ta Kudu. An gina wannan kyawawan makeken gida irin na alfarma a cikin yanayin kwanciyar hankali. An yi ado ga dukkan dakuna 3 da ke cikinsa da kayayyakin daki na gargajiya irin na kasar Sin, kuma dukkan tagogi na fuskanta tabkin.(Tasallah)