Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-22 15:03:02    
Yin yawon shakatawa a dajin itacen gora na Yunding da ke Haiyang na lardin Shandong

cri

A arewa maso gabashin birnin Haiyang na lardin Shandong da ke arewacin kasar Sin, akwai wani dajin itacen gora, sunansa shi ne Yuding. Kullum a kan sami dajin itacen gora a kudancin kasar Sin, amma saboda yanayi, ba safai a kan samu irinsa a arewa ba. Dajin itacen gora na Yunding ya fi girma a arewacin Sin, yanzu ya riga ya zama wurin shakatawa, ya jawo masu yawon shakatawa da yawa da su zo nan don yin ziyara da bincike. Yau za mu kai ziyara ga wannan dajin itacen gora mai suna Yunding tare.

Fadin wurin shakatawa na dajin itacen gora mai suna Yunding ya kai kadada 330 ko fiye, fadin itacen gora ya uwce kadada 60. Tsire-tsire iri daban daban suna girma a nan, itatuwan gingko da na gwanda da suka yi shekaru daruruwa suna nan a wannan dajin itacen gora. Babu tantama gororin da ke zama a ko ina a nan su ne suka fi jawo hankulan mutane.

Mai kula da wurin shatakawa na dajin itacen gora na Yunding malam Li Jinbao ya yi karin bayanin cewa, yau da shekaru sama da 200 da suka wuce, shahararren mai zane marigayi Zheng Banqiao na daular Qing shi ne ya zo Haiyang tare da gorori daga yankunan da ke kudu da kogin Yangtse. Ya dasa su a nan. Zheng ya fi nuna gwanintarsa a fannin yin zane-zane kan gorori, masu kishin zane-zane da yawa sun ajiye zane-zanen da ya yi. A bakin kofar wurin shakatawa na Yunding akwai wani mutum-mutumin da aka yi domin Zheng Banqiao. Malam Li ya ce,

'An rubuta labarin Zheng a cikin littattafai, an kuma amince da shi. Bayan da ya zo nan, Zheng yana ganin cewa, wurin nan wuri ne mai kyau, shi ya sa ya kai gorori a nan daga garinsa, ya dasa su, an kiyaye su, an kuma yi ta fadada su, ma iya cewa, Zheng ya ba mu dukiya mai daraja ta fuskar al'adu. '

Ire-iren gorori 20 ko fiye ana samunsu a dajin itacen gora na Yuding, wasu daga cikinsu muhimmin danyen kaya ne a fannin saka kayayyakin gorori, wasu kuma sun yi suna ne saboda suna saba wa da ko wane irin yanayi. Malam Wang Xuefeng, wanda ke son yawon shakatawa a nan, yana kuma kishin gorori sosai, ya tabo magana kan wata sigar musamman daban ta gororin Yunding, ya ce,

'Ana iya samun irin wannan gora wato Danzhu a kan manyan duwatsun Kunlunshan da na Laoshan a kasar Sin, amma a sauran wuraren arewacin kasar ba safai a kan sami wadanda suka yi girma kamar yadda suke zama a kudancin kasar ba, shi ne wata sigar musamman daban ta dajin itacen gora na Yunding.'

A cikin dajin itacen gora na Yunding, an sami wata gidan ibada mai suna Yunding. Ko da yake ba a san lokacin da aka gina shi ba, amma bisa abubuwan da aka tanada cikin littattafan tarihi, an ce, a zamanin daular Tang, wato yau da shekaru dubu daya ko fiye da suka wuce, masu bin addinin Buddha da yawa su kan zo nan don bautawa addininsu. An ce, wannan gidan ibada wata muhimmiyar tasha ce a kan hanyar zuwa birnin Chang'an, hedkwatar kasar Sin a lokacin can.

A cikin dajin itacen gora na Yunding, yana kasancewa da wani tsohon icen gwanda da ke da tsawon shekaru sama da 300, a idanun mutanen wurin, shi ne ice mai kawo alheri. Malam Xue Qian, ya yi shekaru fiye da 30 yana dasa gorori a matsayin wani ma'aikacin kiyaye dajin. Bari mu ji wata wakar da ya rera game da wannan tsohon ice.

'Taba gindin icen na kare ka daga cuttuttuka, taba jikinsa na kawo maka alheri a zaman rayuwarka, kuma taba rassansa na kawo maka tsawon rai.'

Masu sauraro, bayan da kuka ziyarci dajin itacen gora na Yunding, za ku iya dandano abinci masu dadin ci a nan. Ban da danyun kananan gorori wato bamboo shoot, za ku ci wani irin laman kwadi da ke zama a kan gorori. Miyar da aka yi da kaza abinci ne na musamman da ake samar wa masu yawon shakatawa.

Kazalika kuma, masu yawon shakatawa suna iya yin yawo a kan ruwa cikin kwale-kwalen da aka yi da gorori. Yin kwana a dajin itacen gora na Yunding ya sha bamban da yadda aka yi kwana a cikin otel-otel a birane. Malam Li Jinbao ya ce,

'Yin kwana a babban dutse ya nuna bambanci sosai bisa yin kwana a cikin otel-otel. Kun iya sakin jiki a cikin babban dutsen, dajin itacen gora namu na da matukar kyan gani da dare. Kukan tsuntsaye da karar kwadi da ke kewayenku sun sanya ku ji ku koma karkara.'

Idan masu yawon shakatawa sun kai wa wurin shakatawa na dajin itacen gora na Yunding a lokacin kaka, to, suna iya ganin tsuntsayen pied magpie dubu gomai suna tashi a cikin gandun dajin. Wadannan tsuntsaye su kan zo nan a ko wace lokacin kaka, sun yi wata daya ko daya da rabi suna zama a nan, shi ya sa masu yawon shakatawa mafi yawa sun zo nan a lokacin kaka.(Tasallah)