Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-21 08:56:46    
Kungiyar AU za ta aika manzon musamman don kimanta halin da ake ciki a yankin Darfur

cri
Labarin gidan rediyo na kasar Sin ya ce , a ran 20 ga wata kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta ba da sanarwar cewa, za ta aika da manzonin musamman zuwa kasar Sudan da Chadi da kasar Afirka ta tsakiya domin yin kokarin sassauta hali mai tsanani da ake ciki a yankin da suke ciki sakamakon batun Darfur na kasar Sudan.

Cikin wannan sanarwa, an ce, manzonin musamman na kugiyar tarayya kasashen Afirka guda shida za su tafi kasashen uku cikin wannan mako. Kuma za su kimantar halin da ake ciki a yankin Darfur. Ban da haka, za su binciki yadda ake aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a watan Mayu a tsakanin kasar Sudan da kasar Chadi. Kuma za su nazarci dalilin da ya sa aka dakatar da aiwatar da wannan yarjejeniya. Kuma za su ba da shirin da ya dace ga kokarin daidaita batun da yake kasancewa a wannan yanki daga karshe.(Abubakar)