Jiya an rufe taron shekara shekara na majalisar gwamnonin bankin ADB, wanda aka shafe kwanaki biyu ana yinsa a birnin Shanghai, wanda ya kasance wani birni na zamani da kuma cibiyar kudi ta kasar Sin. Sabo da haka, ni zan kawo karshen ziyarata a birnin, wanda gaskiya ya burge ni kwarai da gaske da kasancewarsa ta zamani da ci gabansa.
Shanghai yana gabashin kasar Sin, fadinsa ya kai muraba'in kilomita 6340.5, kuma yawan mazaunan birnin ya kai million 13 da dubu 681.
Da ma, Shanghai wani dan karamin kauye ne da ke gabar kogin Huangpu, amma ga shi yanzu ya bunkasa har ma ya zamanto cibiyar tattalin arziki mafi girma ta kasar Sin, kuma mashahuriyar tashar jiragen ruwa ta duniya, kuma yana da muhimmin matsayi a fannin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin. Musamman ma bayan da Sin da fara bude kofarta ga kasashen duniya da kuma yin gyare-gyare a shekarar 1978, an kawo wa birnin Shanghai manyan sauye-sauye ta fuskokin tattalin arziki da zaman al'umma. A halin yanzu dai, Shanghai tana kan hanyar zamantowa daya daga cikin cibiyoyin tattalin arziki da kudi da ciniki da sufurin jiragen ruwa na duniya.
Wannan shi ne zuwana na farko a birnin Shanghai, da ma ban taba zuwa ba. Isowata a birnin ke nan, sai wannan birni ya burge ni da tsarinsa da kyaunsa da kuma zamansa na zamani. Ga gine-gine na zamani masu dogayen benaye masu dimbin yawa, ga kuma kyawawan hanyoyi masu fadi, ga shi kuma da bishiyoyi da furanni ko ina. Akwai tsari akwai ci gaba akwai zaman jituwa a wannan birnin. Kasancewar wannan birni cibiyar kudi, gaskiya ta amsa sunansa. Har ma sai ka ce, babban birni ne na zamani a duniya.
An ce, Shanghai birni ne da ba a barci. To, me ya sa? Sabo da wannan birni ya fi nuna kyaunsa da dare. Da dare ya yi, idan an kunna fitilu, sai birnin ya zama wani abin al'ajabi, kuma ka fi iya jin irin albarkar da wannan birni ke da shi. Musamman ma a wani wurin da ake kira "Waitan" wanda ke yammacin gabar kogin Huangpu, inda ke da dimbin gine-gine irin na salon kasashen yammaci. Daga "Waitan" kuma, za ka iya hangen hasumiyar Tv ta Shanghai wadda ke da sunan "Oriented Pearl" wadda kuma ta kasance hasumiyar Tv mafi tsayi ta uku a duniya, tare kuma da babban ginin nan na ake kira "Jinmao", wadanda tamkar alamu ne da suke nuna birnin Shanghai. Daga nan wurin kuma, za ka iya hangen jiragen ruwa masu kyau da ke tafiya a kan kogin Huangpu.
Kasancewar Shanghai birni ne na zamani, amma duk da haka, shi kuma birni ne da ke da daddaden tarihi da kuma al'adu, sabo da haka, da irin wannan halinsa na musamman, yana jawo sha'awar jama'a da kuma masu yawon shakatawa. Har ma ya kasance tamkar wani tauraro ne da ke gabashin duniya.
Sabo da aiki ne ya kawo ni birnin Shanghai, shi ya sa ban sami lokutan yawo a birnin ba, abin da ya rage mini jin dadin wannan ziyarata a birnin ke nan. Amma wannan birni ya burge ni kwarai, shi ya sa nan gaba in Allah ya kai mu, zan sake kawo masa ziyara. Masu sauraro, idan wata rana kun sami damar zuwa kasar Sin, kada dai ku wuce wannan birni mai kyau wanda ba za ku iya mantawa da shi ba. (Lubabatu)
|