Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-18 19:28:15    
Kasar Sin na kokarin yin kwaskwarima a kan aikin kudi na kauyukanta

cri

Yin kwaskwarima a kan aikin kudi na kauyuka wani babban aiki ne da kasar Sin ke fuskanta wajen yin kwaskwarima a kan aikin kudinta. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, hukumomin kula da aikin kudi na kasar Sin sun daidaita manufofinsu game da bai wa bankuna iznin gudanar da harkokin kudi a kauyuka, don ba da taimako ga manoma miliyan 800 wajen samun wadata tun da wuri.

A tsakiyar shekarun 1990, manyan bankunan kasuwanci na kasar Sin daban daban sun janye jikinsu daga kauyuka sannu a hankali, sabo da hadarin rancen kudi da suke damuwa. Ta haka, da kyar manoma su sake samun rancen kudi daga manyan bankuna don bunkasa aikin noma da sauran kananan sana'o'i. Amma yanzu irin wannan hali da manoma ke ciki ya fara sauyawa.

A ran 1 ga watan Maris da ya wuce, an kafa kananan bankuna uku iri na sabon salo da ake kira "bankin kauye" a lardin Sichuan a yammacin kasar Sin da lardin Jilin a arewa maso gabashin kasar. Bisa manufofi da aka tsara, bankin kauyen yana gudanar da harkokinsa ne musamman domin biyan bukatu da ake yi wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin kauyuka. Malam Ding Xiaobo, shugaban kwamitin gudanarwa na babban kamfani mai hannun jari na bankin kauye mai suna Dongfeng na lardin Jilin ya bayyana wa wakilimmu cewa, "bankin kauyenmu yana gudanar da harkokinsa ne domin manoma, don haka muna ba da duk rancen kudi ga manoma musamman domin yin aikin noma da kiwon dabbobi. Makasudin rancen kudi da bankinmu ke bayar shi ne domin taimaka wa manoma wajen samun wadata tun da wuri, da bauta wa aikin raya kauyukan gurguzu na sabon salo."

Ban da bankunan kauyen, kuma an fara kafa kamfanonin ba da rancen kudi maras yawa a kayukan kasar Sin. Yayin da wakilinmu ke neman labaru a wani kauyen gundumar Pingyao na lardin Shanxi da ke arewancin kasar Sin, wani manoma mai suna Wang Zhongqing wanda ya taba samun rancen kudin Sin Yuan dubu 50 daga irin wannan kamfani na kauyensa cikin sauki don kiwon daji, ya bayyana masa cewa, "kamfanin ba da rancen kudi maras yawa ya sami amincewa sosai. A da, ko kusa ba mu iya samun rancen kudi daga tsohuwar kungiyar ba da rancen kudi ta kauyenmu."

Ban da bankunan kauyukan da kamfanonin ba da rancen kudi maras yawa da aka kafa a kauyukan kasar Sin, kuma an kyautata zaton cewa, banki mai suna "China Postal Savings" wanda ya kafu ba da dadewa ba, zai ba da taimakonsa wajen kyautata matsayin gudanar da harkokin kudi domin bautawa manoma. A halin yanzu, bankin yana da rassansa 36,000, daga cikinsu, akwai misalin kashi 70 cikin dari wadanda ke kauyuka. Malam Liu Andong, shugaban kwamitin gudanarwa na bankin "China Postal Savings" ya bayyana cewa, bankinsa zai kafa hukumominsa musamman domin kara bauta wa manoma da kyau a fannin aikin kudi. Ya ce, "bankinsa zai kara kokari wajen kafa tsarin hadin guiwa a tsakanin birane da kauyuka don gudanar da harkokin kudi a duk kasa baki daya."

Kwararru sun nuna cewa, idan ana son kara daga matsayin gudanar da harkokin kudi a kauyukan kasar Sin a tsanake, to, wajibi ne, a tsara manufofin nuna gatanci don sa kaimi ga hukumomin kudi da yawa da su kafa rassansu a kauyuka, da taimake su wajen kara samun kudin jari.

A kan wannan ra'ayi, mallam Liu Mingkang, shugaban hukumar kula da harkokin bankuna ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin za ta yi ta kyautata manufofin kula da harkokin bankuna don ba da taimako wajen bunkasa harkokin kudi a kauyukan kasar. (Halilu)