Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-18 17:43:16    
Yin shawarwari cikin zaman tare cikin lumana hanya daidai ce wajen daidaita batun Darfur

cri
A ran 18 ga wata, lokacin da ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi yake shawarwari da takwararsa ta kasar Ingila madam Margaret Beckett a nan birnin Beijing, Mr. Yang ya ce, yin shawarwari cikin zaman tare cikin lumana hanya daidai ce mai amfani wajen daidaita batun Darfur na kasar Sudan yadda ya kamata.

Mr. Yang ya ce, a cikin halin da ake ciki yanzu, ya kamata bangarori daban-daban su aiwatar da ayyukan shimfida zaman lafiya da na siyasa tare a yankin Darfur cikin daidaito bisa manyan tsare-tsare, da kuma aiwatar da shirin da Mr. Kofi Annan, tsohon babban sakataren M.D.D. ya bayar a kan batu a kai. Kasar Sin tana yin kokarinta a kullum kan yadda za a daidaita batun Darfur yadda ya kamata. Tana son ci gaba da hada da bangarorin da abin ya shafa domin ciyar da ayyukan shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Darfur tun da wuri gaba.

Madam Beckett ta ce, bangaren Ingila tana son kara yin mu'amala da bangaren kasar Sin kan batun Darfur.

Bugu da kari kuma, ministocin kasahen waje sun yi musayar ra'ayoyinsu kan batutuwan da ke da nasaba da gyare-gyaren M.D.D. da neman bunkasuwar Afirka da na Iraki da batun nukiliya na Iran da ayyukan raya Turai bai daya da dai sauransu. (Sanusi Chen)