Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-18 17:41:24    
Gwamnatin birnin Beijijg na himmantuwa wajen yin ayyukan tsaro ga filaye da dakuna na taron wasannin Olympic na Beijing

cri

A duk tsawon lokacin da ake share fage ga taron wasannin Olympic na Beijing da kuma gudanar da shi, wanda yake janyo hankulan mutanen duk duniya, abu mafi muhimmanci da za a yi, shi ne tabbatar da samun kwanciyar hankali a dukan filaye da dakuna na gasanni. Kwanan baya ba da dadewa ba, wani jami'I mai kula da harkokin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya furta, cewa ana yin tsaro da kyau a wuraren gina filaye da dakuna na taron wasannin Olympic na Beijing yayin da ake daukaka ci gaban ayyukan tsaro na bayan ginawar filaye da dakunan wasannin.

Yanzu, a nan birnin Beijing, akwai filaye da dakuna guda 31 na yin gasa, da dakuna guda 45 na horaswa da kuma cibiyar taro ta kasa da dai sauran gine-gine guda 4 dake shafar taron wasannin Olympic. Tabbatar da samun kwanciyar hankali na wadannan muhimman ayyuka don magance aukuwar hadarurrukan hare-haren ta'addanci, ya kasance muhimmiyar dawaiya ce dake gaban kwamitin shirya taron wasanin Olympic na Beijing. Saboda haka, tun da aka soma gina filaye da dakuna na taron wasannin Olympic na Beijing, an kafa wata karamar kungiyar sulhunta ayukan tsaro na taron wasannin Olympic a nan Beijing.

A ran 4 ga watan Afrilu na wannan shekara, an gudanar da taron watsa labarai a game da yanayin tsaro na ayyukan gina filaye da dakuna na taron wasannin Olympic na Beijing a cibiyar watsa labaru ta taron wasannin Olympic na Beijing. Mr. Liu Shaowu, mataimakin darakta na din-din-din na ofishin karamar kungiyar sulhunta ayyukan tsaro na taron wasannin Olympic na Beijing kuma ministan tsaro na kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya yi jawabi a gun taron, inda ya fadi, cewa, makasudin aikin karamar kungiyar sulhunta ayyukan tsaro na taron wasannin Olympic na Beijing, shi ne ' tabbatar da samun kwanciyar hankali a gun taron wasannin Olympic'; Ban da wannan kuma, karamar kungiyar za ta sanya kokari matuka wajen kammala ayyukan gina filin wasan motsa jiki na kasa, wanda ake kiransa ' gidan tsuntsu' wato "bird's nest" a Turance, da dakin wasan iyo na kasar, wanda ake kiransa " dakin wasa mai siffar tafkin wanka" wato " water cube" da dai sauran muhimman gine-gine na zamani, wadanda suke jawo hankulan mutanen duk duniya.

Mr. Liu Shaowu ya kara da, cewa tun bayan da gwamnatin birnin Beijing ta samu iznin gudanar da taron wasannin Olympic na 29, sai aka mayar da ayyukan gina filaye da dakuna na taron wasannin Olympic a matsayin aiki na farko da ke cikin ayyukan share fage ga gudanar da wannan gagarumin taro wasannin. Don haka, tabbatar da samun kwanciyar hankali ga ayyukan gina filaye da dakuna na taron wasannin Olympic shi ma ya kasance dawainiya ta farko dake gaban ayyukan tsaro na taron wasannin.

Jama'a masu saurare, wakilinmu ya samu labari daga taron watsa labaru, cewa domin tabbatar da samun kwanciyar hankali a dukan wuraren da ake gina filaye da dakuna na taron wasannin Olympic, an shigo da wasu fasahohin kimiyya da fasaha da dama cikin ayyukan tsaro na taron wasannin Olympic na Beijing. Alal misali: yanzu ana yin amfani da na'urori na zamani domin sa ido har na tsawon sa'o'i 24 kan muhimman gine-gine da ake yi ; Ban da wannan kuma, an kafa giza-gizan sadarwa na internet domin samun bayanai cikin lokaci a game da yadda ake yin tsaro a wuraren gina filaye da dakuna na wasannin Olympic.

Bisa ayyukan riga-kafi da ake yi a tsanake, ko da yake ma'aikata da wuraren gina filaye da dakuna na wasannin Olympic na Beijing sun yi yawa, wadanda kuma suke da fadi ainun, amma duk da haka, kawo yanzu dai babu wani lamarin aika laifi da ya wakana a cikinsu. Hakan ya tabbatar da samun tsaro mai kyau.

Jama'a masu saurare, gagarumin taron wasannin Olympic na Beijing na kusantowa ; kuma za a kammala ayyukan gina filaye da dakuna na taron wasannin daya bayan daya. An labarta, cewa za a gudanar da jerin gasannin jarrabawa a wannan shekara domin wannan gagarumin taro. Saboda haka ne, mutane suke zura ido sosai kan maganar tsaro na filaye da dakuna na wasannin Olympic na Beijing.

A karshe dai, Mr. Liu Shaowu ya bayyana, cewa bisa dokokin da aka saba tsakanin kasa da kasa da kuma abubuwan da kwamitin wasannin Olympic na duniya, za a yi binciken tsaro ga dukkan 'yan kallo kafin su shiga filaye da dakuna don kallon wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. ( Sani Wang )