Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-18 10:27:44    
Za a kara hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika a fannin kudi

cri

An rufe taron shekara-shekara na majalisar bankin raya Afrika wato ADB a takaice jiya ran 17 ga wata da maraice a birnin Shanghai na kasar Sin. Mr. Zhou Xiaochuan, shugaban majalisar bankin raya Afrika na wannan zagaye kuma shugaban bankin jama'ar Sin ya yi wani jawabi a gun bikin rufe taron, inda ya furta, cewa gudanar da taron shakara-shekara da aka yi tare da nasara, ta samar da wani fadadden dandamali da kuma muhimmin zarafi ga habaka musanye-musanye da hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. Kasar Sin ta lashi takobin kara inganta kyakkyawar dangantakar hadin gwiwa tare da bankin raya Afrika da kuma mara masa baya wajen kara taka muhimmiyar rawa kan yunkurin rage talauci da na raya kasa da ake yi a Nahiyar Afrika.

Jama'a masu saurare, ko kuna sane da cewa, taron shekara-shekara na bankin raya Afrika a shekarar 2007 wanda aka rufe shi ba da jimawa ba, wani taron shekara-shekara ne da wannan banki ya shirya a karo na biyu a waje da nahiyar Afrika, kuma wani gagarumin taro ne da ya gudanar bisa sikeli mafi girma a tarihi. Babban jigon taron, shi ne " Asiya da Afrika abokai ne a fannin raya kasa"; kuma hadin gwiwa tsakanin Asiya da Afrika, wani muhimmin batu ne na taron. Mr. Donald Kaberuka, shugaban bankin raya Afrika ya furta, cewa: " Gudanar da taron shekara-shekara da aka yi a wannan gami tare da nasara zai kara dankon dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasashen Afrika da kasar Sin da kuma tsakanin Afrika da Asiya. Muna cike da kyakkyawan fatan bankin raya Afrika zai kara taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da janyo moriya ga bangarorin biyu sakamakon karuwar cinikayya da zuba jari da ake ta yi".

A daya hannun kuma, Mr. Zhou Xiaochuan ya bayyana, cewa: " Kasar Sin tana so ta kara taka muhimmiyar rawa wajen hadin gwiwar da ake yi tsakanin Asiya da Afrika a fannin kudi. Ban da wannan kuma, gwamnatin kasar Sin za ta kara yin musanye-musanye tare da kasashen Afrika, da kuma kara sanya kokari wajen daukaka ci gaban gyare-gyaren tsarin kudi da ake yi, da kyautata muhallin halittu a fannin kudi da kuma yin musayar fasahohi na kara sarrafa harkokin kudi daga dukkan fannoni. Kazalika, kasar Sin za ta kara sa kaimi ga kamfanonin gida musamman ma wasu kamfanoni da masana'antu masu zaman kansu matsakaita da kanana don su yi bidar damar zuba jari da yin hadi gwiwa a Afrika. Yanzu hukumomin kudi na kasar Sin suna ta kara mai da hankali kan harkokin da suke gudanarwa game da Afrika don kara shiga harkokin raya manyan ayyuka na kasashen Afrika, ta yadda za su samar da hidimomi gare su a fannin raya kasa".

Jama'a masu saurare, a zahiri dai, gwamnatin kasar Sin har kullum takan mai da hankali kan zumunci da hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afrika. Tun bayan da aka shigar da kasar Sin cikin bankin raya Afrika wato ADB a shekarar 1985, har sau 7 ne ta bada kudin karo-karo da yawansu ya kai dola miliyan dari uku da sittin a hudu ga Asusun bada lamuni na Afrika don tallafa wa kasashen Afrika a fannin raya manyan ayyuka da rage talauci da kuma na ilimantarwa.

Domin kara yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika a fannin tattalin arziki da na kudi, bankin jama'ar Sin zai kuma kara shawo kan hukumomin kudi da masana'antun gida masu tarin yawa don su shiga cikin yunkuri hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika. Mr. Zhou Xiaochuan ya fadi, cewa: " Mun tsaya tsayin daka mu kara bunkasa kyakkyawar dangantakar hadin gwiwa tare da bankin raya Afrika; sa'annan za mu ci gaba da tallafa wa kasashen Afrika cikin halin sahihanci wajen rage talauci da raya kasa; dadin dadawa, muna maraba da hukumomin kudi na Afrika don su kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin, wato ke nan su kafa rassa da ofisoshin wakilta na kudi, da sa kaimi ga hukumomin kudi na bangarorin biyu don su nuna himma wajen samo sabon salon da za a bi wajen yin hadin gwiwa a fannin kasuwannin kudi, da hukumomin kudi da kuma na cinikayyar kudi da dai sauransu. ( Sani Wang )