A ran 17 ga wata a birnin Shanghai, shugaban bankin raya Afirka Mr Donald Kaberuka ya bayyana cewa, yana fata kasar Sin za ta kara zuba jari a Afirka.
Mr Kaberuka ya fadi a gun wani taron watsa labaru cewa, yana fata masu zuba jari na kasar Sin da na sauran kasashen duniya za su kara zuba jari a Afirka. Ya ci gaba da cewa, a halin yanzu dai Afirka tana kara samun jari daga kasashen waje, wanda ba a taba ganin irinsa ba a tarihi, wannan yana da kyau ga Afirka. A sa'i daya kuma, Mr Kaberuka yana ganin cewa, Afirka tana bukatar a kara zuba mata jari a fannoni daban daban.
Ban da wannan kuma, Mr Kaberuka yana ganin cewa, babbar matsalar Afirka a fannin muhallin zuba jari ita ce, karancin manyan ayyuka, musamman ma a kan lantarki da dai sauransu albarkatun makamashi. Mr Kaberuka ya ci gaba da cewa, bankin raya Afirka zai kara yin kokari domin kyautata muhallin da ake zuba jari.(Danladi)
|