Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-17 20:13:17    
An rufe taron shekara-shekara na majalisar ADB a Shanghai

cri

Ran 17 ga wata, a birnin Shanghai na kasar Sin, an rufe taron shekara-shekara na majalisar Bankin Raya Afirka wato ADB na shekara ta 2007, wanda aka yi yini 2 ana yinsa. A gun bikin rufe taron, majalisar ADB ta zartas da kuduri, inda ta nuna godiya ga firayim minista Wen Jiabao na kasar Sin saboda ya halarci bikin bude taron, ya kuma ba da jawabi, sa'an nan kuma ta yi wa gwamnatin Sin godiya saboda tana goyon bayan Bankin Raya Afirka da kuma Asusun Raya Afirka wato ADF.

A gun bikin rufe taron, shugaban Bankin Raya Afirka Donald Kaberuka ya yi jawabin cewa, taron shekara-shekara da aka yi a Shanghai taro ne mai muhimmanci sosai a tarihi, kuma taro ne da ya ci nasara. Taron ya tsara 'taswirar hanya' kan bunkasuwar Bankin Raya Afirka. Bankin Raya Afirka zai kara taka muhimmiyar rawa a nan gaba, zai tabbatar da ganin cewa, ciniki da zuba jari da suke wakana a tsaknain Afirka da Asiya za su kawo wa jama'arsu moriyar a-zo-a-gani.

Shugaban majalisar Bankin Raya Afirka a wannan karo kuma shugaban Bankin Jama'ar kasar Sin Zhou Xiaochuan ya ce, Bankin Raya Afirka zai rubanya kokari a fannin rage talauci a Afirka, zai kara sa kaimi kan hada kan Asiya da Afirka, kazalika kuma zai taimaki kasashen Afirka wajen tabbatar da samun bunkasuwa mai dorewa.(Tasallah)