Jiya 16 ga wata, a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin, aka bude taron shekara shekara na majalisar gwamnonin bankin raya Afirka, wato ADB a takaice. A ran nan, wakiliyarmu Lubabatu ta sami damar yin hira da mai girma Alh.Ali Mahaman Lamine Zeine, wanda ke kan kujerar ministan tattalin arziki da kudi na jamhuriyar Nijer, wanda kuma ya kasance daya daga cikin gwamnonin bankin ADB, kuma da sunan jamhuriyar Nijer, kuma ya zo birnin Shanghai ne musamman don halartar taron nan na shekara shekara na majalisar gwamnonin bankin ADB.
Wannan babban taron shekara shekara shi ne karo na farko da bankin ADB ya kira irinsa a kasar Sin har ma nahiyar Asiya baki daya, tun bayan da ya kafu a shekara ta 1964. Lokacin da muka tabo magana a kan abin da ya sa aka zabi kasar Sin aka kira wannan babban taro na ADB, mai girma Ali Mahaman ya ce, dalilin shi ne don nuna dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka baki daya. Kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, kuma Afirka nahiya ce da aka fi samun kasashe masu tasowa, a cewar mai girma Ali Mahaman, Sin da kasashen Afirka suna samun kamanci sosai da juna, ciki har da fama da talauci da neman ci gaba, sabo da haka, shugabannin Sin da Afirka sun hadu a birnin Shanghai don yin musanyar ra'ayoyi da hanyoyi a kan neman ci gaba. "Ita kasar Sin akwai kamanta da yawa cikin al'amuranmu na kasashen Afirka, sabo da kasa ce wadda ta yi kokuwa, ta yi yaki da jahilci, ta yi yaki da talauci, ta nemi ci gaba, duk abin da aka sani, mu ma muna neman mu dauki sawo, mu ga yadda ita wannan babbar kasar Sin ta yi, mu ma mu bi saho, don mu zamanto kasashe masu arziki tun da arziki muna da shi. Ke nan abin ya wakana, kuma sanin juna ya kara tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka."
Hakika kasar Sin ta shiga bankin ADB ne a shekarar 1985, wato yau shekaru fiye da 20 ke nan kasar Sin tana cikin wannan banki na raya Afirka, game da rawar da Sin take takawa cikin bankin, mai girma Ali Mahaman Lamine Zaine ya ce, "Zaman kasar Sin a cikin ADB, bankin ci gaban Afirka, ya sa duka muka yarda, sabo da muna fatan wannan babbar kasa za ta kara kawo goyon bayanta kan sanin da take da shi na ci gaban kasa da kuma kudaden da ake tsammanin za a kara, kuma a bayanta mu ga hanyoyin da ta bi ta fita daga wasu matsalolin da muke da irinsu, sabo da duk wadannan, muka ce, lalle, wannan kasa ta Sin ya kamata ta zamanto tana da wurinta a cikin bankin ADB."
Kasancewarsu kasashe masu tasowa da ke fama da matsaloli iri daya, kullum Sin da kasashen Afirka suna jin tausayin juna da taimakon juna da kuma kaunar juna, musamman ma bayan taron koli na dandalin hadin kan Sin da Afirka da aka yi a birnin Beijing a watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, an kara ciyar da huldar aminci da hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka zuwa wani sabon matsayi. Amma duk da haka, ganin hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ya inganta, wasu sun fito sun ce, Sin tana hadin gwiwa da Afirka ne don neman kwace makamashi da albarkatun kasa na Afirka, kuma abin da take yi a Afirka ya kasance tamkar "sabon salon mulkin mallaka", game da irin wannan furuci, mai girma Ali Mahaman ya yi musun cewa, "wannan ra'ayi nasa ne, su wadanda suka fadi haka yaya suka yi a shekaru 48 a baya, mu abin da muka gani a wannan babbar kasa ta Sin tun da ba wani wayo ne da za a yi wa kasashen, yawancin gwamnatocin da ke kasashen Afirka, kamar mu kasar Nijer kasa ce ta dimokuradiyya, talaka in zai yi zabe ya san wanda zai kada wa kuri'a, ya san wa ya jefa kuri'a, kuma shi ne ke fadi albarkacin bakinsa, ke nan ba ta yiwuwa a ce an zo za zauna a yi mashi wayo ko a mallake shi, wannan abu ne masu hasada ne suka fada haka." (Lubabatu)
|