Jama'a masu sauraro,barkanku da war haka,barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin da kuka saba da sauraronsa na Me Ka Sani Game da Kasar Sin.A cikin wannann shirinmu na yau,za mu cigaba da yi muku bayani kan jam'iyyun siyasa na demakuradiya da suka sa hannu cikin harkokin siyasa na kasar Sin.
Jam'iyyar demakuradiya ta hudu da take taka rawa a cikin harkokin siyasa na kasar Sin ita ce kungiyar bunkasa demakuradiya ta kasar Sin.An kafa wannan kungiyar ne a ran 30 ga watan Disamba na shekara ta 1945.lokacin da aka kafa wannan kungiya,yawancin 'yan kungiyar sun zo ne daga fannonin al'adu da ilimi da dabi da kuma 'yan kasuwa masu kishin kasa na demakuradiya na birnin Shanghai.
A cikin sabon kundin tsarin ka'idoji na kungiyar nan da aka zartas a taron wakilan kasa a karo na tara da aka yi a watan Disamba na shekara ta 2002,an tanadi cewa kungiyar nan tana tafiyar da harkokinta na yau da kullum bisa tsarin mulkin kasa na jamhuriyar jama'ar kasar Sin.Tsarin siyasa na kungiyar nan a matakin farko na zaman gurguzu shi ne bisa jagorancin akidar Deng Xiaoping,kungiyar ta yi nazari da aikata abubuwan da muhimmin tunanin "wakilci a fannoni uku" ya kunsa,ta kammala ayyukanta a kan matsayin jam'iyyar siyasa mai sa hannu cikin harkokin siyasa,ta kuma daga tutar masu kishin kasa da gurguzu sama,ta tsaya tsayin daka wajen aiwatar da babban tafarki na mai da ayyukan raya tattalin arzikin kasa tamkar cibiya da nacewa ga bin manyan ka'idoji guda hudu da kuma yin gyare gyare da bude kofa ga kasashen waje,tana yin gwagwarmayar shimfida zaman jin dadi ga jama'a da mai da kasa ta zama ta zamani da kuma neman dinkuwar kasa da kiyaye zaman lafiya na duniya da gaggauta bunkasuwa tare da kuma mai da kasarmu ta zama kasar gurguzu mai wadata da demakuradiya da wayewar kai.
Har zuwa karshen shekara ta 2005,kungiyar bunkasa demakuradiya ta kasar Sin tana da sassa 302 a matakin yankuna da gundumomi a larduna da jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kansu da birane dake karkashin jagorancin gwamnatin tsakiya kai tsaye 29 da sauran sassan kasa 5806,yawan 'yan kungiyar ya kai dubu 99.
Jam'iyyar siyasa ta demakuradiya ta biyar dake taka rawa a cikin harkokin siyasa na kasar Sin ita ce Jam'iyyar demakuradiya ta manoma da ma'aikata ta kasar Sin.Jam'iyyar nan ta kafu ne a watan Augusta na shekara ta 1930.Mutane masu ilimi mai zurfi ko matsakaici a fannin kiwon lafiya na kasar Sin ne ginshikan jam'iyyar.
Bayan da kasar Sin ta shiga cikin wani sabon mataki,jam'iyyar demakuradiya ta manoma da ma'aikata ta kasar Sin ta karkata hankalinta ga ba da hidima ga ayyukan mai da kasa zaman gurguzu na zamani,ta nuna kwazo da himma wajen shiga harkokin siyasa da sa ido ta hanyar demakuradiya,da bayar da ra'ayoyi da shawarwari ga ayyukan kawo sauyi da bunkasa tattalin arziki da al'adu da na kiwo lafiya,ta ba da taimakonta ga Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da gwamnatin wajen tabbatar da manufofin siyasa game da masu ilimi.'ya'yan Jam'iyyar su kan aza sawunsu a yankuna masu talauci da samarwa dabarun bunkasa tattalin arzikin yankunan da kawo shawarwari da bayar da ilimi bayan aiki da kuma bayar da taimako a fannin ilimi ga yankunan dake dab da iyakar kasa,jam'iyyar ta taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga ayyukan kawo sauyi da bude kofa ga kasashen waje da inganta da bunkasa hadaddiyar kungiyar masu kishin kasa da kiyaye halin siyasa na kwanciyar hankali da hadin kai.
Jam'iyyar demakuradiya ta manoma da ma'aikata ta kasar Sin tana da sassanta a larduna da jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kansu da biranen dake karkashin jagorancin gwamnatin tsakiya kai tsaye su talatin ban da Taiwan da Tibet,'ya'yan jam'iyyar sun kai fiye da dubu tamanin.
|