Labari daga kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya ce, a ran 16 ga wata a birnin Shanghai, shugaban Bankin raya African , ko za a iya tabbatar da dauwamammiyar bunkasuwa a nan gaba ka a'a, wannan ya dogara da fannoni guda shida.
A cikin rahoton da aka gabatar wa taron shekara-shekara na majarlisar Bankin raya African na shekara 2007 da aka bude a ran 16 ga wata, Mr Kaberuka ya ce, karuwar tattalin arzikin da Afika ta samu a cikin shekaru 6 da suka wuce ya kai matakin koli na tarihin Afrika. Duk da haka, ba dukan kasashen Afika ne suke sami karuwar tattalin arziki da sauri ba, ya zuwa yauzu wasu kasashe ba su iya samun karuwar tattalin arziki yadda ya kamata ba.
Mr Kaberuka ya nuna cewa, yauzu, wasu kasashen Afika sun riga sun sami damar tabbatar da dauwamammiyar bunkasuwa. Manyan abubuwa 6 da ke da muhimmanci sosai gare su, su ne: kare zaman lafiya yadda ya kamata; da ci gaba da yin gyare-gyare, da maras canjawar manufa da sauri; da kafa tsari da kwarewa; sarrafa bashi da kyau; da kula da albarkatu yadda ya kamata; da kuma rage kudin da ake kashewa kan raya kan harkokin kasuwanci. (Musa Guo)
|