Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-17 15:45:24    
Ci gaban dangantakar hadin gwiwa ta abokantaka tsakanin Asiya da Afirka yana bukatar kokarinsu tare

cri

A gun taron shekara-shekara na bankin raya Afirka na shekarar 2007 da aka yi ran 16 ga wata, Mr. Zhou Xiaochuan?shugaban majalisar bankin raya Afirka, kuma shugaban bakin jama'ar Sin ya amsa tambayoyin da manema labaru suka yi masa inda ya bayyana cewa, da akwai babban boyayyan karfin da ba a yi amfani da shi ba wajen hadin gwiwa tsakanin Asiya da Afirka, kuma yana da makoma mai haske, aikin bunkasa dangantakar hadin gwiwa ta abokantaka tsakanin Asiya da Afirka zai sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duk duniya baki daya.

Mr. Zhou ya ce, kara bunkasa dangantakar hadin gwiwa ta abokantaka tsakanin Asiya da Afirka yana bukatar kokarin da kasashe daban-daban na Asiya da Afirka za su yi a fannoni 3 wato

Na farko shi ne gudanar da manufar yin ciniki da zuba jari cikin 'yanci da samun iznin shiga kasuwanni cikin gatanci.

Na 2, yin kokarin kyautata muhallin kasuwanci da na zuba jari ta yadda za a kara jawo hankulan kasashen waje da su zuba jari kai tsaye.

Na 3, kara hadi gwiwa tsakanin kasashen Asiya da Afirka wajen kudi. (Umaru)