Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-17 13:01:39    
Gwamnatin kasar Sin tana kokarin daidaita matsalar Darfur ta Sudan cikin lumana

cri

Kwanan baya ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta sanar da cewa, gwamnatin kasar Sin ta tsai da kuduri cewa nan gaba kadan za ta girke sojojin aikin injiniya da yawansu ya kai 275 zuwa shiyyar Darfur ta kasar Sudan, kuma za ta nada wani wakilin musamman kan harkokin Afirka wanda muhimmin aikinsa na yanzu shi ne neman mafitar daidaita matsalar Darfur. Kwararrun kasar Sin kan matsalar Afirka sun bayyana cewa, kudurin da gwamnatin kasar Sin ta tsayar ya bayyana niyyar da kasar Sin ta nuna wajen daidaita matsalar Darfur, wannan yana da amfani ga tabbatar da zaman lafiya na shiyyar Darfur tun da wuri. To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku cikakken bayani game da wannan labari.

Kwanan baya a nan birnin Beijing, madam Jiang Yu, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta bayyana cewa, bisa rokon da sassan da abin ya shafa na M.D.D. suka yi ne gwamnatin kasar Sin za ta girke wata rundunar sojoji aikin injiniya zuwa shiyyar Darfur ta Sudan. Ta ce, "Nan gaba kadan, gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin jirke sojojin aikin injiniya da yawansu ya kai 275 zuwa shiyyar Darfur ta kasar Sudan domin gudanar da shirin mataki na 2 na Annan na M.D.D. dangane da matsalar shiyyar Darfur."

A watan Nuwamba na shekarar 2006, Mr. Kofi Annan, babban sakataren M.D.D. na wancan lokaci ya shelanta cewa, bisa ka'ida ce kasar Sudan ta yarda da M.D.D. da kawancen kasashen Afirka da su girke hadaddiyar rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa shiyyar Darfur. Daga baya kuma, M.D.D. ta aika da mashawartan soja kadan zuwa wannan shiyya domin tafiya da aikinsu na mataki na farko daga cikin matakai 3 wajen girke hadaddiyar rundunar sojan kiyaye zaman lafiya a wannan wuri. A watan Afril na wannan shekara, wakilan bangarori 3 wato M.D.D. da kawancen kasashen Afirka da gwamnatin Sudan sun yarda da aikin gudanar da shiri na mataki na 2 bisa ka'ida, wato M.D.D. za ta kara girke sojoji masu ba da guzuri da aikin injiniya zuwa shiyyar Darfur da kuma ba da gudummawar kiyayyaki ga shiyyar. Shiri na mataki na 3 shi ne, M.D.D. da kawancen kasashen Afirka za su girke wata hadaddiyar rundunar soja wadda yawan mutanenta ya kai fiye da dubu 20 zuwa shiyyar Darfur. Gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin jirke sojojin aikin injiniya zuwa shiyyar Darfur, makasudinta shi ne domin gudanar da shiri na mataki na 2 na M.D.D. da kawancen kasashen Afirka.

Mr. Wang Hongyi, kwararren matsalar Afirka na cibiyar kasar Sin wajen binciken matsalolin kasashen duniya ya bayyana cewa, matakin nan da aka dauka yana da amfani ga tabbatar da zaman lafiya na shiyyar Darfur tun da wuri. Ya ce, "Gwamnatin kasar Sin ta tsai da kuduri cewa nan gaba kadan za ta jirke sojojin aikin injiniya zuwa shiyyar Darfur ta kasar Sudan, wannan ya bayyana niyyar da kasar Sin ta nuna wajen daidaita matsalar Darfur, kuma tana sona yin hadin gwiwa sosai a tsakaninta da kasashen duniya, ta yadda za a sa kaimi ga tabbatar da zama mai dorewa da zaman lafiya na shiyyar Darfur."

Shiyyar Darfur tana yammacin kasar Sudan, sabo da mulkin mallaka da aka cikin tarihi, shi ya sa shiyyar nan ta kasance da sabani iri-iri tsakanin kabilu cikin dogon lokaci, wannan kuma ya haddasa mutuwar fararen hula ko jikata, kuma mutane da yawa sun rasa mazauna.

Madam Jiang Yu ta bayyana cewa, "Kasar Sin kullum tana kokarin daidaita matsalar Darfur yadda ya kamata, ta taba yin wasu ayyukan daidaituwa ta hanyar yin ziyarce-ziyarce ya juna, kuma ta ba da gudummawar jin kai da ta kayayyaki ga shiyyar Darfur da kungiyar musamman da kawancen kasashen Afirka ta aika da ita zuwa shiyyar nan." (Umaru)