A ran 16 ga wata, Zhou Xiaochuan, shugaban majalisar ADB kuma shugaban bankin jama'ar kasar Sin ya yi bayani a birnin Shanghai na kasar Sin, cewa ya yi imanin cewa, za a iya samu ra'ayoyin bai daya a fannoni daban daban da kuma sakamako mai kyau a gun taron shekara shekara na bankin raya Afirka wato ADB.
Lokacin da Mr. Zhou ke zantawa da wakilinmu bayan bikin bude taron, ya bayyana cewa, kira wannna taro cikin nasara zai karfafa muhimmiyar rawa da ADB zai taka wajen rage talaucin da Afirka ke fama da shi da kuma samun bunkasuwa. Kuma zai ci gaba da daga matsayin ADB a fannin ba da hidima ga kasashen Afirka, da kara nuna goyon baya ga Afirka wajen muhimman ayyuka, ta yadda za a iya sa kaimi ga yunkurin bunkasa shiyya-shiyya bai daya.
Ban da wannan kuma Mr. Zhou ya ce, domin inganta hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka wajen tattalin arziki da sha'anin kudi, bankin jama'ar kasar Sin zai karfafa zukatan hukumomin kudi na Sin wajen dora muhimmanci kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. Haka kuma bisa dangantakar aminci da bankin jama'ar kasar Sin da ADB suka kulla cikin dogon lokaci, za a sa kaimi ga hukumomin kudi da kamfanoni masu yawa wajen sa hannu a cikin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka.(Kande Gao)
|