Ran 16 ga wata, a birnin Shanghai na kasar Sin, an bude taron shekara-shekara na kwamitin Bankin Raya Afirka na shekara ta 2007. A gun bikin bude taron, firayim minista Wen Jiabao na kasar Sin ya bayyana cewa, gwamnatin Sin za ta sabunta tunanin yin hadin gwiwa a tsakaninta da Afirka da daga matsayin hadin gwiwarsu don tabbatar da samun moriyar juna da ci nasara tare.
Taron shekara-shekara da aka bude a yau karo ne na 2 da Bankin Raya Afirka wato ADB ya shirya a sauran wurare, kuma karo na farko ne da ya yi a Asiya. An mayar da 'Afirka da Asiya abokai ne wajen samun bunkasuwa' a matsayin babban takensa, inda za a dora muhimmanci kan yin tattaunawa kan muhimman ayyuka a Afirka da dinkuwar Afrika gu daya da kuma kawar da talauci. A gun bikin bude taron, shugaban Bankin Raya Afirka Donald Kaberuka ya yi bayanin cewa,'Asiya da Afirka sun kulla huldar tattalin arziki a tsakaninsu cikin dogon lokaci, sun kuma sami saurin bunkasuwa wajen raya irin wannan hulda a cikin shekaru 5 da suka wuce. A matsayinta na kasuwa mafi samun saurin ci gaba a duniya, bunkasuwar Asiya ta kawo wa Afirka kalubale, haka kuma ta kawo mata dama da karfin gwiwa. Wannan taron shekara-shekara na samar da zarafi a gare su wajen yin mu'amalar fasahohi masu kyau da kuma kyautata huldar aminai a tsakaninsu.'
Firayim minista Wen Jiabao ya nuna babban yabo ga bude wannan muhimmin taron, ya ce,'A matsayinsa na muhimmiyar hukumar kudi ta shiyya-shiyya, a cikin shekaru fiye da 40 da suka wuce, Bankin Raya Afirka yana yin kokari ba tare da kasala ba wajen sa kaimi kan raya kasashen Afirka ta fuskar tattalin arziki da zaman al'ummar kasa, ya kuma sami sakamako mai kyau. A cikin shekaru 2 da suka shige, ya yi gyare-gyare, ya nemi samun sabbin hanyoyi a fannin kara bai wa kasashen Afirka hidimomi masu kyau. Tabbas ne wannan taron shekara-shekara zai ci gaba da sa kaimi kan raya Bankin Raya Afirka da kara karfafa amfaninsa da tasirinsa.'
Ko da yake a shekarun baya da suka wuce, kasashen Afirka sun sami babban ci gaba wajen raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasa, amma Mr. Wen yana ganin cewa, Afirka na bukatar ci gaba da yin kokari da kansu don kara samun ci gaba, sa'an nan kuma, tana bukatar goyon baya da tallafi daga kasashen duniya.
A matsayinta na daya daga cikin kasashen duniya, har kullum kasar Sin tana taimakawa kasashen Afirka cikin himma da kwazo. Firayim ministan Sin ya bayyana cewa, ya zama wajibi ne Sin da Afirka su sabunta tunani a fannin yin hadin gwiwa a tsakaninsu, da daga matsayin hadin gwiwarsu don tabbatar da moriyar juna da ci nasara tare. Ya ce,'Sin za ta bi hanyoyi 2 tare don cimma burinta, wato ba da taimakonta da kuma sa kaimi kan hada kai a tsakanin masana'antu, za ta jagoranci masana'antu da su yi hadin gwiwa bisa tsarin kasuwa. Za ta kara mai da hankali kan gudanar da ayyukan jin dadin jama'a, musamman ma muhimman ayyuka domin al'umma, da aikin gona da kiwon lafiya da ba da ilmi da rage talauci da kiyaye muhalli, wadanda jama'ar Afirka ke maraba da su. Kazalika kuma, za ta dora muhimmanci kan yin hadin gwiwa ta fuskar fasaha da horar da kwararru da taimakawa kasashen Afirka don kyautata karfin samun bunkasuwa, za ta kuma ba da taimako bisa ka'idojin kasa da kasa a fili cikin adalci yadda ya kamata.'
Ya kara da cewa,'Hada kan Sin da Afirka wani bangare ne na yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen duniya domin samun bunkasuwa, gwamnatin Sin tana son ci gaba da kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da sauran kasashe da hukumomin kudi na kasa da kasa, wadanda suka hada da Bankin Raya Afirka, za su yi kokari tare domin samar wa Afirka kyakkyawar makoma da sa kaimi kan raya duniya mai jituwa da zaman lafiya cikin dogon lokaci da kuma wadatuwa tare.'(Tasallah)
|