Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-16 18:01:28    
Tarihin bankin din nan na ADB, wato African Development Bank

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Alh.Musa Abubakar, wanda ba mu tabbatar da wurin da ya fito ba, sabo da bai bayyana ba. A cikin wata wasikar da ya turo mana, ya ce, ina son a ba ni tarihin bankin din nan na ADB, wato African Development Bank. To, jama'a masu sauraro, domin amsa tambayar, a cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku takaitaccen bayani a kan bankin nan na raya Afirka, wato ADB.

A watan Yuli na shekarar 1963, a birnin Khartoum, babban birnin kasar Sudan, an yi taron manyan jami'ai da masana na Afirka tare kuma da taron ministocin kasashen Afirka, inda aka cimma wata yarjejeniya dangane da kafa bankin raya Afirka, wato African Development Bank a bakin Turawa, ko kuma ADB a takaice. Sa'an nan a shekarar 1964, a hukunce ne bankin ya kafu. Daga baya, a ran 1 ga watan Yuli na shekarar 1966, bankin raya Afirka ya fara gudanar da harkokinsa.

Da ma, hedkwatar bankin raya Afirka yana birnin Abidjan, amma sakamakon yakin basasa da ya auku a kasar Cote d'Ivoire a watan Satumba na shekarar 2002, an dauke hedkwatar bankin zuwa kasar Tunisiya. Babbar manufar bankin ita ce, zuba jari da samar da rancen kudi da kuma yin amfani da kwararru da albarkatun kasa na Afirka, don sa kaimin bunkasa tattalin arzikin kasashe mambobin bankin, sa'an nan, bankin zai fi samar da kudade da taimakon fasaha ga ayyukan da za su amfana wa hadin gwiwar tattalin arzikin shiyyar da kuma habaka cinikin da ke tsakanin kasashe mambobinsa. Bayan haka, bankin zai kuma yi nazari da kuma tsara wa kasashen Afirka daban daban shirin bunkasa tattalin arzikinsu, ta yadda za a cimma bunkasuwar tattalin arzikin Afirka bai daya.

Majalisar gwamnonin bankin raya Afirka ita ce hukumar koli ta bankin, kuma ko wane mamban bankin na da wani gwamna a cikin majalisar, wadanda su kan kasance ministan kudi ko na tattalin arziki. Kwamitin ya kan kira wani taro a ko wace shekara, inda a kan zabi shugaban bankin da kuma shugaban darektoci, inda kuma a kan tattauna da kuma tsara manufofin bankin da yanke shawara kan manyan batutuwan bankin. Bayan haka, majalisar gwamnoni ta kuma kula da zaben majalisar darektoci, wadda ta kasance hukumar zartaswa ta bankin, wadda kuma ta kan kula da harkokin yau da kullum na bankin. Shugaban majalisar darektoci shi ma ya kasance shugaban bankin.

A halin yanzu dai, bankin raya Afirka na da mambobi 77, kuma 53 daga cikinsu kasashe ne na nahiyar Afirka, sauran 24 kuma kasashe ne da ba na Afirka ba, ciki har da kasar Sin, wadda ta shiga bankin a shekarar 1985.

Bayan haka, bisa wani labarin da muka samu da dumi-duminsa, an ce, nan gaba ba da dadewa ba, wato daga ranar 16 zuwa 17 ga watan nan da muke ciki, za a yi taron shekara shekara na majalisar gwamnonin bankin nan na raya Afirka a birnin Shanghai na kasar Sin, wanda zai kasance wani muhimmin taron kasa da kasa da Sin za ta kira bayan taron koli na dandalin hadin kan Sin da Afirka da aka yi a birnin Beijing a watan Nuwamba na shekarar da ta wuce. Babban jigon wannan taro shi ne "Afirka da Asiya, abokai ne wajen neman ci gaba", kuma a gun taron, za a fi tattauna raya manyan ayyukan Afirka da bunkasuwar shiyyar bai daya da kuma saukaka fatara da sauransu, kuma ana sa ran firaministan kasar Sin, Wen Jiabao zai halarci bikin bude taron da kuma bayar da jawabi.(Lubabatu)