Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-16 17:45:00    
Wani mai bauta wa addinin Buddah kuma mai yin zane-zane na zamanin yau na kasar Sin mai suna Shi Guoliang

cri

Malam Shi Guoliang da ke sanya rigar addinin Buddah shi ne mutumin da ke da sha'awa sosai. Ya yi zane-zane cikin tsanaki bayan da ya yi nazari sosai kan akidojin addini, shi kuma bako shehun malami na sassan koyar da fasahohin yin zane-zane na jami'o'I da yawa a kasar Sin.

Mr Shi Guoliang da ke da shekaru 51 da haihuwa a shekarar da muke ciki shi ne mashahurin mai yin zane-zane kan sifoffin mutane na zamanin yau na kasar Sin kafin ya bi akidojin addinin Buddah . Zane-zanen da ya yi kan sifoffin mutane sun bayyana yadda jama'ar farar hula suke zaman rayuwa a yau da kullum, kamar zane-zanen da ya yi kan yadda manoma suke girbin alkama irin na jihar Tibet, wato Qingke ke nan, da kuma wata macen da ke aikin dinki a farfajiyar gidanta tare da tsuntsaye da dabboin gida nata da wadanda suke saye da sayarwa a kasuwar kauye, dukkan wadannan sun bayyana halin da ake ciki na yin zaman rayuwa cikin farin ciki sosai.

Tun lokacin da yake karami, yana son yin zane-zane, a shekaru 70 na karnin da ya shige, ya taba koyon fasahar yin zane-zanen gargajiyar kasar Sin daga manyan malaman yin zane-zanen gargajiyar kasar Sin masu sunaye Zhou Sicong da Huang Zhou.ya kasance da bambanci sosai a tsakanin zane-zanen kasashen yamma da na gargajiyar kasar Sin. Ana yin zane-zanen gargajiyar kasar Sin ta hanyar yin amfani da alkalami da takardu da ruwan tawada na musamman kawai, malamansa guda biyu suna saba yin zane-zane kan sifoffin mutane, wannan ya ba da tasiri sosai ga Shi Guoliang wajen yin zane-zanensa. Har wa yau dai a lokacin da ya waiwayi abubuwa dangane da malamansa guda biyu, sai ya ci gaba da ji cewa, sun burge shi sosai da sosai, ya kuma ji alheri sosai saboda shi ne dalibansu. Ya bayyana cewa, Na yi alfahari sosai saboda zamana ya kasance cikin irin wannan zamani mai kyau, manyan malamaina dukkansu suna da rai a duniya, shi ya sa na kafa ingantaccen tushe wajen yin zane-zane. Har wa yau dai na yi farin ciki sosai da samun manyan malamai masu yin zane-zane na kasar Sin wadanda su da kansu suka koyar mini fasahohin yin zane-zane, saboda haka na ji dadin zamana sosai. Kuma matsayina wajen yin zane-zane ya kara daguwa

A shekaru 80 na karnin da ya wuce, Mr Shi Guoliang ya taba dalibta a kasashen waje, ya koyi fasahohin yin zane-zane na kasashen yamma cikin shekaru kusan goma. A shekarar 1995, a gun wani shagalin dare da aka shirya don neman taimako ga jama'a, wani mai bautawar dakin ibadan Addinin Buddah ya gaya wa Mr Shi Guoliang cewa, Ga fuskarsa kamar yadda ya yi kama da wani mai bautawar addinin Buddah a dakin ibada, sai nan da nan ya fahimci makomarsa ta nan gaba. Ya bayyana cewa, abin da wannan mai bautawa addinin Buddah ya fada ya shiga zuciyata sosai da sosai har da hawaye, a wancan lokaci, na mai da hankali sosai ga amincewar addinin, ina son zaman rayuwar masu bauta wa addinin Buddah sosai.

A shekarar 1995, da gaskiya ne ya aske gashin kansa ya shiga gidan masu bauta wa addinin Buddah, daga nan sai Mr Shi Guoliang yana da ayyuka guda biyu, wato yin zane-zane da nuna biyyaya ga addinin Buddah. Ya ce, kodayake ya riga ya zama wani mai bautawa addinin Buddah, amma ya yi fatan zai ci gaba da ba da gudumuwarsa ga jama'a da zamantakewar al'umma. Ya ce, makasudina wajen zama wani mai bautawa addinin Buddah shi ne ba domin kubutar da ni daga wahaloli kawai ba, sai kuma ina son gaya wa mutane abubuwan da na ji na gani wajen kubutar da ni daga wahaloli, duk saboda mutane suna kan samun matsalolin da suke dame su sosai, ya kamata zan taimake su ta hanyar kubutar da kansu daga wadannan wahaloli.(Halima)