Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-16 10:26:56    
Sin da Afrika suna tattaunawa a kan hadin guiwarsu don moriyar juna da samun bunkasuwa tare

cri

A ran 16 ga wata, a birnin Shanghai na kasar Sin, an fara yin taron shekara-shekara ta 2007 na majalisar rukunin bankin raya Afrika da za a shafe kwanaki biyu ana yinsa. Mambobin bankin da suka fito daga kasashe 77 za su halarci taron shekarar nan. Babban batu da jami'an kasar Sin da na kasashen Afrika da masanan ilmin tattalin arziki da masu masana'antu mahalartan taron ke sha'awar tattaunawa a kai, shi ne yadda za a kara inganta hadin guiwa a tsakanin Sin da Afrika don moriyar juna, da gaggauta raya bangarorin biyu musamman kasashen Afrika da kyau kuma cikin sauri. Wakilan gidan rediyon kasar Sin sun kai ziyara ga shahararrun mutane na Afrika don jin ta bakinsu a kan wannan batu. To, bismilla:

Yayin da Malam Victor Kidiwa, shugban bankin kasar Kenya wanda ke halartar taron shekara-shekarar nan ya bayyana wa wakilanmu cewa, "matsalar da kasar Kenya ke fuskanta a yanzu a fannin tattalin arziki ita ce, yadda za ta kara jawo kudin jari mai yawa daga kasashen waje musamman ma kudin jari da kasashen waje za su zuba wa kasar kai tsaye don taimakawa jama'arta wajen raya kasarsu. Muna zura ido ga jama'ar Sin da za su zuba jari a kasar Kenya, kuma su kai mata sakamako da suka samu wajen raya kasa. Mun yi imani cewa, jama'ar kasar Kenya za su ci gajiyar hadin kan kasashen Kenya da Sin."

Alhaji Isyaku Ibrahim wani dan masana'antu ne da ya fito daga kasar Nijeriya. Ya gaya wa wakiliyarmu cewa, yana fata zai samu damar hadin kansa da kasar Sin ta hanyar taron shekara-shekarar nan da ake yi yanzu a kasar Sin. Yana ganin cewa, masana'antun Afrika za su sami fa'ida daga wajen hadin kan Sin da Afrika. Ya ce, "kasar Sin babbar kasa ce. Sabo da haka muna sha'awar inganta hadin kai da harkokin tattalin arziki da ciniki a tsakaninmu da kasar Sin. Akwai abubuwa da yawa na kasar Sin da muke son mu yi koyi da su. Sa'an nan kuma ta hanyar hadin kanmu, za mu iya musanya wa juna abubuwa da muke da su, mu sami manyan kasuwannin kasar Sin."

A lokacin da Malam Ashraf El Leifhy, babban editan kamfanin dillancin labaru na gabas ta tsakiya na kasar Masar ya karbi ziyarar da wakilnmu ya kai masa, ya bayyana cewa, birnin Shanghai na kasar Sin ya sauke nauyin shirya wannan taron shekara-shekara na bankin raya Afrika. Wannan ya shaida cewa, yanzu ana nan ana tabbatar da sakamako sannu a hankali da shugabannin kasashen Sin da na Afrika suka samu a gun taron koli na Beijing da aka yi a shekarar bara. Ya kara da cewa, "a watan Nuwamba na shekarar bara, shugaban kasar Sin ya gabatar da matakai 8 cikin basira don yin hadin kan Sin da Afrika bisa manyan tsare-tsare har cikin dogon lokaci, ana cin gajiyar matakan nan sosai wajen yin hadin kansu bisa halin da ake ciki yanzu. Bisa wadannan matakai ne, za a yi taron shekara-shekarar nan. Taron da za a shirya a kasar Sin a karo na farko shi ma sakamako ne ga taron koli na Beijing."

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, an yi ta kara inganta dangantakar tattalin arziki da ciniki a tsakanin Sin da Afrika. Sabo da haka kara inganta hadin kansu a fannoni daban daban buri ne iri daya ga bangarorin nan biyu kuma bukatu ne da suke yi. Hajiya Amina Ibrahim, mai ba da taimako ta musamman ta shugaban kasar Nijeiya mai kula da shirin bunkasuwa na shekaru 1000 da ke halartar taron shekara-shekarar nan ta bayyana wa wakiliyarmu cewa, "kasar Sin tana da tattalin arziki mai girma sosai. Sabo da haka wasu mutane suna nuna damuwa a kan hadin kan Sin da Afrika. Amma a ganinmu jama'ar Afrika, kasar Sin tana da abubuwa da muke bukata, sa'an nan muna da abubuwa da kasar Sin ke bukata, don haka muna taimakon juna ne, mu iya bunkasa ma'amalar tattalin arziki da ciniki a tsakaninmu." (Musa Guo)