Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-16 07:56:57    
Shugaban kwamitin wasannin Olimpic na nakasassu na duniya ya gamsu da aikin shirya taron wasannin Olimpic na nakasassu na Beijing

cri

Masu sauraro,kamar yadda kuka sani,birnin Beijing yana yin iyakacin kokari domin shirya taron wasannin Olimpic na shekarar 2008,a sa`i daya kuma,yana yin aikin share fage domin shirya taron wasannin Olimpic na nakasassu na shekarar 2008.Kwanakin baya ba da dadewa ba,Mr.Philip Craven,shugaban kwamitin wasannin Olimpic na nakasassu na duniya ya kai ziyara a birnin Beijing domin yin aikin rangadi kan aikin shirya taron wasannin Olimpic na nakasassu da za a yi a birnin a shekarar 2008.Bayan da ya kammala aikin rangadi a birnin Beijing,Mr.Craven ya yabawa aikin da birnin ke yi sosai.A cikin shirinmu na yau,bari mu yi muku bayani kan wannan.

An haifi Mr.Craven a shekarar 1950,yayin da shekarunsa da haihuwa suka kai 16,ya gamu da wani hadarin hawan dutse,ya zama wani gurgu,daga nan kuma ya fara wasan kwallon kwando kan kujera mai taya.Daga shekarar 1972 zuwa shekarar 1988,gaba daya sau biyar ne ya shiga gasar wasan kwallon kwando kan kujera mai taya ta taron wasannin Olimpic na nakasassu.Saboda haka,Mr.Craven yana ganin cewa,abu mafi muhimmanci ga aikin shirya taron wasannin Olimpic na nakasassu shi ne aikin ba da hidima ga `yan wasa wato kamata ya yi a mayar da bukatun `yan wasa a gaban kome.Mr.Craven ya ce, `Na dauka cewa,abu mafi muhimmanci shi ne a mayar da bukatun `yan wasa a gaban kome,haka kuma `yan wasa za su nuna matsayinsu yadda ya kamata.Dalilin da ya sa haka shi ne domin `yan wasa suka yi kokari suka sha wahalhalu masu tsanani da shekaru hudu domin shiga taron wasannin Olimpic na nakasassu,shi ya sa dole ne a shirya musu gine-gine mafiya inganci,musamman dakunan wasanni da cibiyoyin wasanni.Ban da wannan kuma,kauyen `yan wasa wato wuri mai daukan `yan wasa shi ma yana da muhimmanci sosai,alal misali dakin kwana da abinci.`

Ko birnin Beijing ya riga ya biya dukkan wadannan bukatu?

Mr.Craven yana ganin cewa,sharadin sufuri yana da muhimmanci kwarai da gaske ga gasannin da za a shirya,game da wannan,kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing ya riga ya kafa wata hanyar musamman domin taron wasannin Olimpic na nakasassu wanda za a yi a shekara mai zuwa,tsawonta ya kai kilomita 235,Mr.Craven ya ji dadi kan wannan.

Ban da wannan kuma,Mr.Craven ya dauka cewa,gine-gine masu saukin hawa ga nakasassu za su kawo babban tasiri ga taron wasannin Olimpic na nakasassu.Ya ce,  `Game da gine-gine masu saukin hawa ga nakasassu,kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing ya yi kokari kuma aikin shirya da yake yi ya fi sauran kasashe.Ko shakka babu,shirya taron wasannin Olimpic na nakasassu a birnin Beijing zai sa kaimi ga gwamnatin birnin wajen gina gine-gine masu saukin hawa ga nakasassu.`

Kazalika,Mr.Craven shi ma ya tabo magana kan dakin wanka da ake gina a cikin dakunan saukan `yan wasa nakasassu,`yan wasa suna iya shiga dakin wanka kan kujera mai taya.Ya fayyace cewa,a gun taron wasannin Olimpic na Beijing,shi kansa da sauran `yan wasa dubu 4 za su hawa babbar ganuwa bisa taimakon gine-gine masu saukin hawa ga nakasassu.

Mr.Craven ya bayyana cewa,a gun ziyarar da ya yi a cikin kwanaki 6 da suka shige a birnin Beijing,ya tabbatar da cewa,ya gamsu da aikin share fage na fannoni daban daban da kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na nakasassu na birnin Beijing ke yi sosai,alal misali,wuraren gasanni da sharadin sufuri da gine-ginen filin jirgin sama da sauransu.Ya ce,yanzu dai ana yin kokari don tabbatar da zaman jituwa a duk fadin kasar Sin,a karkashin irin wannan hali,ko shakka babu,birnin Beijing zai shirya wani taron wasannin Olimpic na nakasassu dake cike da al`adu tare da cikakkiyar nasara.Ya ce, `Taron wasannin Olimpic na nakasassu dake cike da al`adu ya yi daidai da tunanin shugaban kasar Sin Hu Jintao wato zaman jituwa.A shekarar 2005,na taba ganawa da firayin minista Wen Jiabao a babban dakin taron jama`ar kasar Sin,shi ma ya cike da imani kan taron wasannin Olimpic na nakasassu.Ana zura ido kuma ana fatan taron wasannin Olimpic na nakasassu da za a yi a birnin Beijing a shekara mai zuwa zai samu cikakkiyar nasara.`

To,jama`a masu sauraro,karshen shirinmu na yau ke nan,ni Jamila da na gabatar nake cewa,ku zama lafiya,sai makon gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Jamila Zhou)