Jama'a masu sauraro, barkanku da war haka, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin, wanda mu kan gabatar muku a ko wace ranar Talata. Kamar yadda muka saba yi, da farko dai, za mu karanta muku wasu abubuwa kan shiyyar kabilar Zang ta Diqing mai ikon tafiyar da harkoki da kanta, daga bisani kuma, sai wani bayanin musamman mai lakabi haka 'Ni'imtattun wurare masu ban mamaki a kwarin da ke tsakanin manyan duwatsu mai suna Zhangbu a Guizhou'.
Shiyyar Diqing ta kabilar Zang mai ikon tafiyar da harkoki da kanta tana arewa maso yammacin lardin Yunnan na kasar Sin, ta hada da gundumomi 3 wato Shangri-La da Deqing da kuma Weixi. 'Yan kabilun Zang da Han da Bai da Naxi da Yi da Hui da Pumi da Lisu da kuma Miao suna zaman tare cikin jituwa a wannan yanki mai fadin murabba'in kilomita 23,870. Cikin kwanciyar hankali ne ake bin addinai iri daban daban, kamar su addinin Buddha irin na kabilar Zang da na Confucianism da Tao da Katolika da Musulunci da Bon da kuma Dongba.
Wannan shiyya wuri ne mai ni'ima kuma mai dogon tarihi da kyakkyawan wayin kai. Wurin tarihi na zamanin tun can can da da aka gano a Geden na gundumar Weixi ya nuna cewa, mutane sun fara zama a nan yau da shekaru misalin dubu 7 da suka wuce. Akwatunan jana'iza na dutse da aka ajiye a jikin manyan duwatsu da sauran wuraren tarihi da aka samu a gundumar Deqing sun shaida cewa, kakan kakanin Diqing sun taba samar da kyawawan al'adu. Hanyar kasuwanci da aka bi a zamanin da don jigilar shayi da doki, wato hanyar siliki ta kudancin kasar Sin ta ratsa Diqing, wadda ta taba taka muhimmiyar rawa a fannin kasuwanci saboda ta hada kasar Sin da kasashen India da Nepal har ma da duk nahiyar kudancin Asiya.
Kyawawan ni'imtattun wurare masu ban mamaki su ne suke jawo masu yawon shakatawa da yawa da su kai ziyara ga Diqing. A tudun Diqing, sun iya hawan manyan tsaunukan Meili da Baimang da Haba da Balagengzong, wadanda kankara mai taushi ke rufe kansu. Babbar kololuwar tsaunin Meili wato Kagebo ita ce kololuwa mafi tsayi a duk lardin Yunnan, wadda kuma daya ce daga cikin manyan duwatsu 8 masu muhimmanci a cikin zukatan 'yan kabilar Zang. Ban da wannan kuma, sauran wurare masu ni'ima sun hada da kogin Jinshajiang da mafarin kogin Yangtze da kogin Lancangjiang da tabkin Bitahai da gidan ibada na Songzanlin da dai makamantansu. Abin da ya fi jawo hankulan masu yawon shakatawa shi ne wuri mai suna Shangri-La, inda dan Adam da halittu ke zaman tare, ana shimfida jituwa a nan.
|