Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-15 18:41:17    
Kamfanonin kasar Sin, abokai ne na fararen hula na Sudan

cri
A cikin shekaru masu dimbin yawa da suka wuce, kamfanonin kasar Sin wadanda suke aiki a kasar Sudan sun samu amincewa daga wajen jama'ar kasar domin suna kokari da kuma nuna sahihanci ga jama'ar kasar Sudan. Yanzu, wadannan kamfanonin kasar Sin sun riga sun zama aminan jama'ar Sudan.

A shekarar 1996, kamfanin samar da ayyukan ban ruwa da karfin wutar lantarki na kasar Sin ya kafa wasu tasoshin daga ruwa da hanyoyin ban ruwa ya isar da ruwan kogin Nil a cikin unguwannin fararen hula na kasar Sudan wadanda suke zama a cikin hamadar Sahara, sabo da haka, ya warware matsalar ban ruwa da ta taba kasancewa a gabansu. Filin hadamar Sahara da fadinsa ya yi yawa ya zama filin tsire-tsire. A cikin ofishin Mr. Wang Peng, wato babban direktan sashen kamfanin samar da ayyukan ban ruwa da karfin wutar lantarki na kasar Sin da ke kasar Sudan, akwai wata takardar nuna yabo. Mr. Wang ya gaya wa wakilinmu cewa, "Manoman wurin ne sun ba mu wannan lambar yabo da wani buhu na alkama bayan da suka girba sakamakon yin amfani da tsarin ban ruwa da muka yi musu. Sun gaya mana cewa, wannan alkama ne da suka samu sakamakon isowar ruwa a cikin gonakinsu ta tsarin ban ruwa da muka yi."

Mr. Sun Zhongyu, babban injiniya ne na sashen kamfanin shigi da ficin injuna na kasar Sin da ke kasar Sudan ya bayyana cewa, tun daga shearar 1996 zuwa yanzu, kamfaninsa ya riga ya gina kananan tasohin rarraba wutar lantarki 8 a kasar Sudan. Kowace tasha tana samar da wutar lantarki ga kauyukan da ke cikin yankin da fadinsa ya kai murabba'in kilomita dari 1. Sabo da haka, mazaunan wurin suna farin ciki sosai, kuma su da kansu ne su kan samar da taimako ga kamfanin kasar Sin. "Kafin mu soma gina karamar tashar rarraba wutar lantarki ta 2 a kasar Sudan, mun nemi ruwa a wurare da yawa. Mun kuma haka rijiyoyi 3 domin neman ruwa, amma ba mu samu kome ba. A wani kauyen da ke nesa da mu da kilomita kimanin 5 ko 6, akwai wata husumiyar samar da ruwan sha. Mutanen wannan kauye su da kansu ne suka zuba ruwa a cikin tankinmu, sannan sun isar da wannan tanki a wurin da muke zama, amma ba su karbi kudi ko kobo guda ba."

Tun daga shekarar 2005, kamfanin ZTE da kamfanin Huawei na kasar Sin sun gama aikin kafa wani tsarin CDMA a kasar Sudan a cikin rabin shekara kawai. Sabo da haka, sana'ar sadarwa ta kasar Sudan ta samu cigaba cikin sauri. Mr. Tian Feng, direktan sashen kula da harkokin kasuwanni na kamfanin ZTE da ke kasar Sudan ya ce, "A cikin kusan shekara 1 kadai, yawan sabbin masu yin amfani da tsarin CDMA da muka yi a Sudan ya kai miliyan 1 da dubu dari 5. Galibinsu sun yi amfani da wayar salula a cikin karo na farko ne. Mutane fararen hula na Sudan suna jin dadin yin amfani da na'urorin wayar salula da muka samar."

Lokacin da suke yin hadin guiwa da musaye-musanye a tsakaninsu a cikin dogon lokacin da ya wuce, jama'ar Sin da na Sudan sun kara samun fahimtar juna a tsakaninsu. Mr. Zhou Shangmin, babban direktan kamfanin CCMD JV na kasar Sin da yake gida madatsar ruwa ta Marwi, wato ayyuka mafi girma na samar da wutar lantarki a kasar Sudan ya ce, "Dukkan jama'ar Sudan suna da kirki sosai. Lokacin da suka gan ka, sai su ce 'Sadiq' daga nesa. Wannan dalili daya ne da ya sa ina son kasar Sudan. Bayan da muka yi hadin guiwa da jama'ar Sudan a kan wannan ayyuka a cikin dogon lokacin da ya wuce, ya yi tasiri mai kyau ga zumunci da musanye-musanyen al'adu a tsakaninmu."

Yanzu, kamfanonin kasar Sin fiye da 90 suna aiki a kasar Sudan. Ayyukan da suke yi suna da nasaba da man fetur da wutar lantarki da madatsar ruwa da tagwayen hanyoyin mota da tasoshin ruwa da sadarwa. Lokacin da suke cimma kwangiloli iri iri a kasar Sudan, suna kuma kokarin kyautata sharudan jiyya da makarantu a wurin. Malam Muatazz nasr Adlan ya riga ya yi shekara fiye da 1 yana aiki a cikin wani asibitin da kamfanonin kasar Sin suka gina a kasar Sudan ya ce, "A cikin wannan asibiti, na samu cigaba sosai. Na warkar da marasa lafiya da yawa, karfina na yin aikin jiyya ma ya samu kyautatuwa. Ina farin ciki sosai domin ina aiki a wannan asibiti tare da 'yan uwa na kasar Sin."

Malam Bakri Mulah, babban sakataren kwamitin Sudan mai kula da harkokin yada labaru ga kasashen waje ya ce, "kamfanonin kasar Sin sun bayar da gudummowa sosai wajen ciyar da tattalin arzikin kasar Sudan gaba. Kasar Sin tana samar mana taimako ba tare da kowane sharadi ba. Bangarorin biyu suna yin hadin guiwa ne bisa tushen siyasa na girmama wa juna da moriyar juna da ba su tsoma baki cikin harkokin gida nasu." (Sanusi Chen)