A ranar 16 ga wannan wata a birnin Shanghai, majalisar rukunonin bankin raya Afrika za ta kira taro na shekarar 2007 cikin kwanaki biyu. Babban batun da za a yi a gun taron shi ne, Afrika da Asiya su ne abokan neman bunkasuwa. Wannan ne karo na farko da bankin raya Afrika ta shirya taron shekara shekara a wata kasar Asiya.
Wannan taron bankin raya Afrika da bankin jama'ar kasar Sin da gwamnatin birnin Shanghai suka shriya shi ne taron kasashen duniya daban da kasar Sin ta shirya a kan batun kasashen Afrika bayan taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a shekarar da ta shige. Shugaban bankin raya Afrika Mr Donald Kaberuka ya karbi ziyarar da wakilin gidan rediyo kasar Sin ya yi masa, ya yi maraba da kasar Sin saboda ta shirya taron. Ya bayyana cewa, ma'anar taron tana shafar wuri da lokaci da za a shirya shi. Yanzu, huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika tana kasancewa cikin lokaci mai muhimmanci. Kira taron ya samar da sarari ga kara kyautata huldar. Kasar Sin kasa ce da ta sami bunkasuwa da saurin gaske a duniya, sa'anan kuma kasuwa ce da ta sami bunkasuwa da saurin gaske. Zuwanmu a kasar Sin shi ne don ganin yadda kasar Sin ta samu irin bunkasuwa da idonmu na kanmu, muna son kara inganta huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika bisa manufar da aka tsara a gun taron koli na dandalin tattaunawa kan batun hadin guiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Afrika.
Bankin raya Afrika da aka kafa a shekarar 1964 shi ne hukumar raya harkokin kudi mafi girma a Afrika a tsakanin gwamnatocin shiyyar nan. Daga cikin mambobi 77 da ke cikin bankin nan, da akwai kasashe 53 na Afrika tare da kasashe 24 da ke waje da shiyyar wadanda suka hada da kasar Sin da Japan da Korea ta Kudu da Indiya da sauran kasashe. An kira taron bankin nan na shekarar da muke ciki bisa sharudan da kamfannoni sai kara yawa suke yi da kuma shiga ayyukan raya kasashen Afrika. Labarin da muka samu daga kasashen Afrika ya bayyana cewa, Nahiyar ASiya ta riga ta zama babbar abokiyar kasashen Afrika ta uku wajen yin cinikayya bayan nahiyar Turai da kasar Amurka. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kasar Sin da kasar Indiya da sauran kasashen Asiya suna ta kara zuba jari kai tsaye bisa babban mataki a kasashen Afrika . A gun taron shekarar da muke ciki, mahalartan taron za su tattauna kan wasu batutuwan da suka jawo hankulansu tare bisa babban batun taron. Tun daga shekarar 1995 har zuwa yanzu, tattalin arziki na kasashen Afrika ya yi ta samun bunkasuwa da kashi 3 cikin dari a shekaru 12 a jere . Tattalin arziki na kasashen Afrika yana nan yana shiga lokaci na samun bunkasuwa mai dorewa cikin zaman karko. Mr Kaberuka yana ganin cewa, kasashen Afrika sun sami bunkasuwar tattalin arziki bisa taimakon jarin da kasar Sin da sauran kasashen waje suka zuba kai tsaye. Mr Kaberuka ya bayyana cewa, an kimanta cewa, jarin da kasar Sin ta zuba wa kasashen Afrika zai kai kudin Amurka da yawansu zai kai dolla biliyan biyu a kowace shekara, bankin raya Afrika ya yi fatan zai yi ganin kara samun karuwar jarin da kasar Sin za ta zuba. A cikin shekaru 6 da suka wuce, yawan kudaden da aka samu daga cinikayya a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ya karu da ninki 5 ko fiye, bankin raya Afrika ya yi fatan huldar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika za ta ci gaba da samun bunkasuwa, kuma bankin yana son kara ba da taimako ga raya huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.
A sa'I daya kuma, Mr Kaberuka ya bayyana cewa, yanzu lokaci ne mafi kyau da za a zuba ga kasashen Afrika. Ya kirayi masu zuba jari ciki har da masana'antun kasar Sin da su kara fannonin zuba jari a kasashen Afrika, ya bayyana cewa, a cikin shekaru 6 da suka wuce, tattalin arzikin kasashen Afrika ya sami bunkasuwa da ba a taba gani ba . Mun kirayi abokan kasashen Afrika da su tafi Afrika don neman sararin samun bunkasuwa, amma ba wajen man fetur da gas da ma'adinai kawai ba, a wajen sauran fannoni, kasashen Afrika su ma suna iya samar da sararin aiwatar da harkokin kasuwanci.(Halima)
|