Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-14 21:35:08    
Wani jami'in ADB ya ce, yanzu ana nan ana rage yawan hadarurrukan da ake samu wajen zuba jari a Afrika

cri
Yau 14 ga wata a birnin Shanghai, Mr. Timothy Turner, daraktan sashen bankin raya kasashen Afrika, wato ADB ya ce, ga masu zuba jari na kasashen duniya, ciki har da masana'antun kasar Sin, yanzu ana nan ana rage yawan hadarurrukan da ake samu wajen zuba jari a Afrika.

Mr. Turner ya ce, Afrika wani yanki ne da aka fi samun hadarurruka a da, sabo da haka, bai iya jawo jari da yawa daga kasashen waje ba a cikin dogon lokaci. Manyan hadarurrukan da aka samu a Afrika su ne, hadarurrukan ciniki da hadarurrukan da ba na ciniki ba, inda ya hada da hadarin siyasa da dai sauransu.

Mr. Turner ya bayyana cewa, rahotanni kan kimantawar hadarurruka masu sarkakiya da ake yi a yanzu a Afrika ya nuna cewa, muhallin zuba jari na Afrika ya samu kyautattuwa a shekaru 3 da suka wuce, ana nan ana rage hadarurruka wajen zuba jari. (Bilkisu)