Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-14 19:25:39    
Kasar Sin tana fatan sakamakon da aka samu daga wajen zumuncin da ke kasancewa tsakanin Sin da Afirka zai moriyar jama'ar Afirka

cri
A ran 14 ga wata a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan nuna goyon baya ga farfaduwa da bunkasuwar Afirka. Tana son kara yin mu'amala da daidaituwa a tsakaninta da kasashen Afirka ciki har da kasar Rwanda domin za a iya tabbatar da ganin cewa, sakamakon da aka samu daga wajen zumuncin da ke kasancewa tsakanin Sin da Afirka zai moriyar jama'ar Afirka gaba daya.

Lokacin da yake yin shawarwari tare da takwaransa na kasar Rwanda Paul Kagame wanda ke yin ziyara a kasar Sin, Mr. Hu ya ce, bangaren Sin yana son hada kan bangaren Rwanda wajen karfafa dangantakar siyasa da hadin guiwa a fannonin cinikayya da zuba jari da aikin gona da ayyukan yau da kullum da ke tsakaninsa da kasar Rwanda domin kara ciyar da dangantakar da ke tsakanin Sin da Rwanda gaba. A waje daya, bangaren Sin yana son kara yin musaye-musaye da hadin guiwa a fannonin ilmi da al'adu da kiwon lafiya da wasannin motsa jiki a tsakaninsu. Sannan kuma, Mr. Hu ya ce, kasar Sin tana son kara yin hadin guiwa da daidaituwa da kasar Sin a hukumomi da kungiyoyin kasa da kasa.

A cikin nasa jawabin, Mr. Kagame ya ce, bangaren Rwanda yana fatan kara yin hadin guiwa da bangaren Sin a kan batutuwan kasa da kasa da kuma yin hadin guiwa bisa ka'idojin taron dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afirka. Yana da imani cewa, aiwatar da sakamakon da aka samu daga wajen taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afirka zai kara ciyar da tattalin arzikin Afirka gaba. Bugu da kari kuma, ya bayyana cewa, kasar Rwanda za ta ci gaba da bin ka'idar kasancewar Sin daya tak a duniya. (Sanusi Chen)