Jiya Asabar, gwamnatin Sudan ta yi marhabin da nadin wakilin musamman kan lamuran Afrika da kasar Sin ta yi saboda a cewarta matakin nan ya shaida, cewa gwamnatin kasar Sin za ta bada karin taimako wajen warware maganganun Afrika ciki da batun Darfur.
Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sudan ya fadi, cewa manzon musamman na kasar Sin ba wai zai kula da batun Darfur ba, a'a shi ma zai sa lura kan sauran maganganun Afrika da kuma bada taimako wajen daidaita su.
Sa'annan kakakin ya yi nuni da, cewa ya kasance da kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen Sudan da Sin. Kuma gwamnatocinsu za su ci gaba da yin shawarwari kan batun Darfur da kuma sauran batutuwa. ( Sani Wang )
|