Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-14 08:50:48    
An kafa Asusun bunkasuwa na Sin da Afirka

cri

A ran 13 ga wata a birnin Shanghai, Mr. Gao Jian, mataimakin shugaban bankin raya kasar Sin ya ce, kwanan baya, gwamnatin kasar Sin ta riga ta amince da kafuwar asusun bunkasuwa na Sin da Afirka wadda ke daya daga cikin matakai 8 da gwamnatin kasar Sin ta dauki alkawarin kafuwarta lokacin da aka yi taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin guiwa tsakanin Sin da Afirka. Bankin raya kasar Sin ya kuma riga ya gabatar da "Shirin kafa asusun bunkasuwa na Sin da Afirka".

Mr. Gao ya fadi haka ne a gun taron tattaunawa mai lakabi "Bude kofar sha'anin kudi ga kasashen waje da hadin guiwar Sin da Afirka" domin share fagen taron shekara-shekara na majalisar bankin raya kasashen Afirka na shekara ta 2007 a birnin Shanghai na kasar Sin. Bisa shirin da bankin raya kasar Sin ya bayar, a farkon kafuwar wannan asusu, yawan kudadenta zai kai dalar Amurka biliyan 1, sannan za a kara yawan girmanta har ya kai dalar Amurka biliyan 3, daga karshe dai, yawan kudadenta zai kai dalar Amurka biliyan 5. Muhimman ayyukan wannan asusu su ne, zuba jari kan takardun hannun jari da kwarya-kwaryar takardun hannun jari da sarrafa kudaden da ake zubawa da ba da shawara kan yadda za a zuba jari. A waje daya, za ta kara nuna goyon baya ga aikin gona da sana'o'in kira da sana'ar makamashin halittu da na sadarwa da na zirga-zirga da raya ayyukan yau da kullum a birane na kasashen Afirka tare da masana'antun kasar Sin wadanda suke neman bunkasuwa a kasashen Afirka. (Sanusi Chen)