|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2007-05-14 17:51:39
|
Shugaban kasar Cape Verde ya iso birnin Shanghai don halartar taron shekara-shekara na majalisar ADB
cri
Yau 14 ga wata da safe, shugaba Pedro Verona Pires na kasar Cape Verde ya iso birnin Shanghai, kuma zai halarci taron shekara-shekara na majalisar bankin raya kasashen Afrika, wato ADB na shekarar 2007 da za a shirya daga ran 16 zuwa ran 17 ga wata a birnin.
Shugaba Pires zai yada zango har na kwanaki 5 a birnin Shanghai. Zai yi shawarwari na bangarori biyu tare da firayin ministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao, kuma zai halarci bikin bude taron shekara-shekarar da kuma sauran aikace-aikace. (Bilkisu)
|
|
|