Jama'a masu sauraro assalam alaikum,barkanku da wannan lokaci barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan fili na duniya ina labari.A cikin shirinmu na yau za mu kawo muku wani bayanin da wakilin gidan rediyonmu ya kawo mana kan wani kamfani na kasar Sin wanda ya kawo haske ga kasar Sudan.
A makekiyar hamada dake arewa da birnin Khatoum,babban birnin kasar Sudan, wata babbar hasumiyar karfe mai launin azurfa na tsaye a kan hamada wanda ya hada da hanyoyin samar da wutar lantarki na kasar Sudan.Kamfanin gina tasoshin samar da wutar lantarki na Harbin na kasar Sin ne ya dau nauyin shimfida hanyoyin samar da wutar lantarki a kasar Sudan
Kamfnin Harbin na kasar Sin ne ya dau nauyin gina tashar Garri ta samar da wutar lantarki ta kasar Sudan wadda ta fi girma daga cikin tasoshin ba da lantarki da ke yin amfani da karfin ruwa.Tashar Garri,aikin hadin kai tsakanin kasar Sin da Sudan wajen samar da wutar lantarki,kuma ayyuka ne mafi girma na samar da wutar lantarki a kasar Sudan.Mataimakin shugaban kamfanin Harbin na kasar Sin a Sudan Mr Xu Hong ya bayyyana cewa "tun daga shekara ta dubu biyu ne kamfaninmu ya hada gwiwada kasar Sudan wajen gina tashar Garri a mataki na farko.Mun kammala aiki yadda ya kamata,tashar ta fara samar da wutar lantrki kafin watanni takwas bisa shirin da aka tsara.Bayan da tashar da muka gina ta fara aiki,yanayin samar da wutar lantarki ga birnin Khatoum ya samu kyautatuwa sosai,wutar lantarki da tashar da muka gina ta samar a shekrar bara ya kai kashi 35 cikin kashi dari na daukacin lantarki da aka samar a duk fadin kasar Sudan."
Ban da wannan kuma kamfanin Harbin na kasar Sin ya dau nauyin ayyukan samar da wutar lantarki na madatsar ruwa ta Marwi da ya fi kasaita daga irinsu a Afrika a halin yanzu da sanya hanyoyin wutar lantarki da tsawonsu ya kai kilomita 1776 da manyan taoshi bakwai na rarraba lantarki ta yadda za su hada da tashar Garri su samar da lantarki ga duk kasa baki daya.da haka mutanen Sudan na daukar kamfanin Harbin "manzon musamman da ya kawo haske".
Har zuwa yanzu da akwai ma'aikatan kamfanin Harbin na kasar Sin 3500 da suka shiga ayyukan samar da wutar lantarki a kasar Sudan.lalle su fuskanci matsaloli da dama da wuyan a siffanta su.Wani injiniya mai suna Wei Yong da ya je Sudan a shekara ta 2000,ya ce ba ya saba da yanayin kasar Sudan a farkon saukarsa a wannan kasa.Ya gaya wa wakilinmu cewa " da na sauka a kasar Sudan ban saba da yanayin wannan kasa ba.babu gidajen zama masu kyau sai wasu tantuna da akwatuna na daukar kaya.kuma babu abin sanyaya yanayi a ciki,lalle mun sha wahala sosai.haka kuma babu abinci mai kyau sai dankalin turawa da tattasai da kuma abubuwan da ake kira radish a turance kawai.haka kuma babuwa ruwa mai tsafta sai mun yi amfni da inji don tantance su. Da wuya na shiga barci a kowace rana da dare a farkon saukarna."
Da ya ke ya sha wahala a aikinsa cikin shekaru takwas da suka gabata,kansa ya kara wayewa,ya gane muhimmancin da aikinsa ke da shi da kuma muhimmancin taimakon kasashen Afrika da ke fama da talauci.Ya ce a ko ina a kasar Sudan mutanen kasar Sin na iya jin karimci da aminci da kuma girmamawa da mutanen Sudan ke nuwa musu.Malami Ali Muhammad wanda ya yi aiki da takwaransa na kasar Sin a kamfanin ya yi alfahari da cewa "ni mutumin ne da ya fi dadewa a aikin kamfanin kasar Sin.Kamfanin Sin ya ba da kyakkyawar alama gare ni.na tattara fasahohi da dama wajen aiki.na saje da mutanen Sin,wannan ba karo na farko ba ne na yi aiki a kamfanin kasar Sin,na yi wani kamfanin Sin daban kafin shekaru uku da suka gabata.babu tantama tashar Garri ta taka rawar gani ga ayyukan samar da wutar lantarki na kasar Sudan haka kuma ta taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da ayyukan masana'antu da noma na kasar Sudan gaba.kafuwarta ta kawo sauran ayyuka a yankin kewayenta kamar su hanyoyin mota da asibiti da kuma makarantu.kafuwarta kuma za ta bayar da karin dama ga kasar Sudan wajen samun babban cigaba.
Bayan da aka kammala ayyuka a mataki na farko,tashar Garri ta fara samar da wutar lantarki,an samu sassaucin samar da wutar lantarki a yankin babban birni na Khatoum.Tattalin arzikin kasar Sudan na samun saurin cigaba saboda tana da isashiyar wutar lantarkin da take bukata.Gwamnatin kasar Sudan na sa ran cewa tattalin arzikin kasa zai yiwu ya karu da kashi 13 cikin kashi dari a wannan shekara da muke biki.
Jama'a masu sauraro,wannan dai ya kawo karshen shirinmu na yau na duniya ina labari.mun gode muku saboda kuka saurarenmu.(Ali)
|