Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-13 18:05:44    
Bankin raya kasa na Sin yana son gama kai da hukumomin kudi na raya kasa na Afirka

cri

A ran 13 ga wata a birnin Shanghai, mataimakin shugaban bankin raya kasa na Sin Mr Gao Jian ya bayyana cewa, hukumomin kudi na raya kasa na shiyya shiyya kamar bankin raya Afirka da dai sauransu suna taka muhimmiyar rawa a Afirka, bankin raya kasa na Sin yana son gama kai da su a fannoni daban daban.

A ran nan kuma a birnin Shanghai, an shirya taron kara wa juna sani a kan raya kasa da kudi da kuma gama kan Sin da Afirka a fannin tattalin arzki, wanda bankin raya kasa na Sin ya dauki nauyin shirya shi. A gun taron, Mr Gao Jian ya fadi cewa, a matsayin hukumar kudi ta raya kasa ta gwamnatin kasar Sin, bankin raya kasa na Sin zai ci gaba da rike da babban makasudinsa wato samun moriyar juna da bunkasuwa tare, zai ci gaba da nuna goyon baya ga manyan ayyukan da gwamnatocin Afirka suke mai da hankali a kai, bankin raya kasa na Sin kuma zai kara yin mu'amala da gama kai da hukumomin kudi da dai sauransu hukumomin gwamnatocin Afirka ta hanyar kasuwanci.(Danladi)