A ran 13 ga wata a birnin Shanghai, mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin Mr Wei Jianguo ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari tare da kasashen duniya, domin taimakawa Afirka da ta kara kwarewarta wajen samun bunkasuwa da kansu.
A gun taron kara wa juna sani a kan raya kasa da kudi da kuma gama kan Sin da Afirka a fannin tattalin arzki da aka shirya a ran nan, Mr Wei ya ce, bunkasuwar tattalin arzikin duniya bai daya tana samar da wata kyakkyawar damar samun bunkasuwa ga kasa da kasa, wadda ba a taba ganin irinta ba a tarihi, amma a sa'i daya kuma ta kawo kalubale ga bunkasuwar Afirka. Idan babu zaman karko da wadatuwa a Afirka, to, ba za a iya samun zaman lafiya da bunkasuwar duniya ba. Sabo da haka, ya zama tilas ne kasashen duniya su kara mai da hankali a kan kokarin da kasashen Afirka suke yi domin samun zaman karko da bunkasuwar tattalin arziki a shiryyarsu, kuma su dauki hakikanan matakai domin taimakawa Afirka da su warware matsalolinsu a yayin da suke neman samun bunkasuwa, wadannan matsaloli sun hada da basussuka masu yawan gaske da talauci da karancin manyan ayyukan zaman rayuwa da dai sauransu.(Danladi)
|