Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-11 16:02:58    
Babbar madatsar ruwa ta Marwi ta kasance tamkar wani sabon abin inshara na zumuncin dake tsakanin kasashen Sin da Sudan

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, babbar madatsar ruwa ta Marwi dake arewancin kasar Sudan, babbar tasha ce ta biyu dake samar da wutar lantarki mai aiki da karfin ruwa da ake ginawa kan reshen kogin Nile, kuma wani babban aiki ruwa da na lantarki ne mafi girma da ake yi yanzu a kasar Sudan har a fadin duk yankin Afrika. Ana daukar wannan babbar madatsar ruwa a matsayin ci gaban yunkurin sada zumunta tsakanin kasashen Sin da Sudan ; haka kuma ta kasance tamkar wani sabon abin inshara ne na zumuncin da ke tsakaninsu.

An labarta, cewa a ran 20 ga watan Mayu na shekarar 2003, wani hadadden kamfanin raya ayyukan tsare ruwa da samar da lantarki na kasar Sin wato CCMD JV ya samu cimma burin samun kwangilar daukar nauyin gina wannan babbar madatsar ruwa ta Marwi. Babban manajan kamfanin wato Mr. Zhou Shangmin ya furta, cewa: " Kogin Nile, wani kogi ne mafi tsawo a duniya; kuma babbar madatsar ruwa ta Marwi, wata babbar madatsar ruwa ce mafi tsawo da muke ginawa kan wannan kogi, wato tsawonta ya kai kusan kilo-mita goma sha daya, wadda za ta yi babban tasiri ga kasar Sudan."

Sa'annan Mr. Zhou ya bayyana, cewa yawan ruwan da za a adana cikin babbar madatsar ruwa zai kai ninkin-mita biliyan goma sha hudu bayan an gina ta. Kuma mutane samar da miliyan uku za su ci gajiya daga wajenta. A lokaci daya kuma, aikin gina wannan babbar madatsar ruwa zai samar da aikin yi ga farar hula na wurin da yawansu ya zarce miliyan ashirin da biyar. Yanzu, an rigaya an kammala akasarin ayyukan gina madatsar ruwan yayin da aka kammala ayyukan gina hanyoyin mota, da makarantu, da asibiti da kuma filin jirgin sama dake kewayanta, wadanda aka shafe shekaru kasa da hudu kawai ana gina su. Wani injiniya mai suna Halid Ahamed na kasar Sudan ya gane wa idonsa sauye-sauyen zaman rayuwarsa sakamakon ginawar wannan babbar madatsar ruwa. Ya yi farin ciki da fadin, cewa : " Ko shakka babu, za a samu manyan sauye-sauyen zamantakewar al'mmar duk yankin nan bayan an kammala gina wannan madatsar ruwa mai kayatarwa. Lallai da kyar a siffanta wahalhalun da muka sha kafin wannan lokaci. Amma yanzu muna zaman jin dadi. Ga fadin gonaki na kara habakawa, kuma ana kara samun saukin daukar ababen hawa ; dadin dadawa, an riga an warware maganar karancin wutar lantarki daga doron kasa. Na hakkake, cewa za mu kara samun kyakkyawar makoma a nan gaba'.

Jama'a masu saurare, yanzu akwai ma'aikata sama da dubu biyu da dari hudu na kasar Sin da suke aiki ba dare ba rana tare da ma'aikatan Sudan. Wadannan ma'aikata suna jurewa wa yanayin zafi, da bala'in guguwar iska da kura, da na cizon sauro har da raunuka da sukan samu wajen aiki.

Ana kiran wannan babbar madatsar ruwa ta Marwi a kan cewa " Babbar madatsar ruwa ta San Xia" ta Sudan. Gwamnatocin kasashen Sin da Sudan suna sa lura sosai a kai. Kansulan tattalin arziki da kasuwanci na ofishin jakadancin kasar Sin dake Sudan Mr. Hao Hongshe ya fadi, cewa : " Babu tatama babbar madatsar ruwa za ta taka muhimmiyar ruwa ga yunkurin bunkasa tattalin arzikin kasar Sudan. Idan an kammala gina ta, to za a iya samun kilo-watts miliyan daya da dubu dari biyu da hamsin maimakon dubu dari shida da wani abu kawai a da. Hakan zai rubanya karfin lantarki da duk kasar Sudan take da shi".

Ban da wannan kuma kansula Hao ya yi nuni da ,cewa hadin gwiwa dake tsakanin kamfanonin kasashen Sin da Sudan, hadin gwiwa ne da ake yi domin kawo zaman alheri ga jama'ar kasashen biyu bisa tushen daidaiwa daiwa da samun moriyar juna .

Mr. Bakri Mulah, babban sakataren majalisar kula da harkokin farfaganda ga ketare ta Sudan ya jaddada, cewa lallai kasar Sudan ba za ta iya kammala wannan babban aiki muddin ba ta samu taimako daga kasar Sin ba. ( Sani Wang )