Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-11 14:53:33    
Kasar Sin ke ci gaba da inganta da kyautata tsarin tattalin arzikinta daga manyan fannoni

cri

Kasar Sin tana bunkasa harkokin tattalin arzikinta cikin sauri a shekarun nan da yawa da suka wuce a jere, kuma kasar za ta ci gaba da yin haka a shekarar nan. A cikin watanni biyu na farkon shekarar nan, kasar Sin ta kara samun babban ci gaba wajen bunkasa aikin masana'antu da cinikayyar waje da sauransu. Amma kasar ta gamu da matsaloli da sabane-sabane masu yawa a fannin tattalin arzikinta. Sabo da haka kasar Sin za ta ci gaba da inganta da kyautata tsarin tattalin arzikinta daga manyan fannoni.

A ran 18 ga watan Maris da ya wuce, a karo na uku ne babban banki na kasar Sin ya daga yawan ruwan kudi da ake ajiyewa a bankunan kasar. Malam Chen Yulu, shugaban kolejin koyon aikin kudi na Jami'ar Jama'ar kasar Sin ya bayyana cewa, makasudin daga yawan ruwan kudi da ake ajiyewa a bankunan kasar a wannan gami, shi ne domin sassauta makudan rancen kudi da ake ta kara bayarwa. Ya ce, "wata muhimmiyar alama da aka samu daga wannan mataki da babban bankin na kasar ya dauka ita ce, idan ba a iya sarrafa kudaden jari masu yawa har fiye da kima da ake amfani da su ba, kuma ba a iya sassauta makudan rancen kudi da ake bayarwa ba, to, mai yiwuwa ne, bankin zai kara daga yawan ruwan kudin da ake ajiyewa a bankunan kasar."

A gun taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da aka shirya a watan Maris da ya wuce, Mr Wen Jiabao, firayim ministan kasar ya bayyana cewa, a shekarar nan, za a daidaita jimlar rancen kudi da ake bayarwa a kasar Sin yadda ya kamata ta hanyoyin aiwatar da manufofi game da harkokin kudi. Sa'an nan za a sassauta kudaden jari masu yawa har fiye da kima da ake iya amfani da su yadda ya kamata. Kazalika gwamnatin kasar Sin za ta kayyadde yawan kudin jari da ake zubawa a kan kaddarori.

Malam Wang Jian, babban sakataren cibiyar nazarin ilmin tattalin arziki a manyan fannoni ta kasar Sin ya bayyana cewa, "idan masu masana'antu sun gano ribar kudi da suke iya samu a wani fanni, to, tabbas ne, za su kara zuba kudin jari mai yawa a kai. Amma idan dukanninsu sun yi haka, to, mai yiwuwa ne, kayayyaki da suke fitarwa za su yi rara har ba za a iya sayar da su gaba daya ba. Ta haka yawan ribar kudi da suke samu ba zai gamsar da su kamar yadda suka yi a shekarun baya ba. A hakika dai, mun gano cewa, ribar kudi da suke samu daga masana'antu da ake kara zuba kudin jari mafi yawa a kai ya ragu."

Bisa kimantawar da ofishin bincike na babban bankin kasar Sin ya yi, an ce, a shekarar nan, saurin karuwar yawan kayayyaki da kasar Sin ke fitarwa zai ragu. Amma yawan kudin musanya da kasar Sin ta tanada ya riga ya wuce dalar Amurka biliyan 1,000 a yanzu. Ko da yake tanadin isasshen kudin musanya yana taimaka wa kasar Sin wajen sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin kasar, amma mai yiwuwa ne, karuwar kudin musanya da kasar ke tanada cikin sauri zai haddasa rikicin kudi. Yanzu, daga cikin kudaden musanya da kasar Sin ta tanada, dalar Amurka ta fi yawa. Bisa babban sharadi da ba za a kawo tasiri ga dalar Amurka da ta tanada ba, kasar za ta kafa kamfanonin zuba jarin kudaden musanya musamman domin tanadin kudaden musanya da zuba jarinsu ta hanyoyi daban daban. Malam Jin Renqing, ministan kudi na kasar Sin ya bayyana cewa, "kasar Sin za ta kafa kamfanonin zuba jarin kudaden musanya wadanda ke karkashin shugabancin majalisar gudanarwa ta kasar, za ta yi koyi da sakamamko da kasashen waje suka samu a wasu fannoni, don kula da harkokin zuba jarin kudaden musanya, ta yadda za a kara samun riba da moriya wajen yin amfani da kudaden musanya da ta tanada lami lafiya kuma yadda ya kamata."(Halilu)