Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-10 18:17:51    
Massar ta nuna himma sosai kan sa kaimi ga warware rikicin Darfur na Sudan ta hanyar siyasa

cri

Labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua da ke a Ciro ya aiko mana a ran 9 ga watan Mayu ya ce,Massar ta nuna himma kan sa kaimi ga warware rikicin Darfur na Sudan ta hanyar siyasa.

A cikin kwanakin nan,Massar ta nuna himma sosai wajen harkokin waje, don bayyana matsayin da ta dauka kan batun Darfur na Sudan,kuma ta gabatar da sabon shirin warware batun Darfur,don sa kaimi ga warware batun Darfur ta hanyar siyasa.

A ran 9 ga wata,ministan kula da harkokin waje na Massar Ahmed Abul Gheit ya isar da sako a baka ga ministocin kula da harkokin waje na Majarisar Dinkin Duniya da Kawancen Afrika da Tarayyar Turai da kuma zaunanun kasashe biyar na kwamintin sulhu na M.D.D, inda ya gabatar da sabon shirin warware batun Darfur na Sudan.Sabon shirin nan yana kunshe da abubuwa da yawa kamar su saka gudanarwar siyasa ta Darfur ta ci nasara a karkashin jagoracin M.D.D da Kawancen Afrika,sa kaimi ga kungiyoyi masu yawa da keyin adawa da gwamnati domin su amince da wadda gwamnatin Sudan ta kulla tare da wani mihimmin rukuni na masu yin adawa da gwamnati ta Darfur a watan Mayu a shekarar bara,don tabbatar da zaman lafiya a duk fannonin.

Ban da wannan kuma, Ahmed Abul Gheit ya nuna cewa,shirin da Massar tana gabatar ta kunshe ne da jadawalin daddale yarjejeriyar shimfida zaman lafiya tun da wuri tsakanin gwamnatin Sudan da kungiyoyi masu yin adawa da gwamnati da matakan nuna yabo da yin hukunci.A sa'i daya,Massar ta yi kira ga a yi wani babban taron da yankuna da sassan da abin ya shafa na kasashen duniya za zu halarta,don neman samun goyon bayan shirin.Ban da haka,Massar ta yanke shawarar kafa ofishin wakilin diplomasiya a yankin Darfur,don mai da hankali sosai ga halin da ake ciki a Darfur.(Amina)