Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-10 09:57:11    
Bayani kan Jam'iyyar Kwaminis ta Sin (babi biyu)

cri

Ka'idar tsare tsaren da jam'iyyar ke bi ita ce: ta hanyar zabe a boye a samu wakilan jam'iyya da 'yan kwamiti na mataki daban daban.Kowace kungiya ko kowane mutum na jam'iyyar bai kamata su tilasta wani da ya yi zabe ko ya zabe wani.Idan a sami batun da ya saba wa tsarin ka'idoji na jam'iyyar wajen zaben 'yan majalisu ko wakilan sassa na jam'iyyar a mataki daban daban,ya kamata sassan sama na jam'iyyar ya tsai da kuduri mara amfani da sakamakon zabe ko ya dauki mataki gwargwado bayan da ya yi bincike da tabbatar da shi,haka kuma sassan kasa ya ba da rahoto kan batun nan ga sassan sama,bayan da sassan sassan sama na jam'iyyar suka zartas da shi,sassan kasa na jam'iyyar na iya aiwatar da shi.Kwamitin tsakiya na jam'iyyar da kwamitocinta dake mataki daban daban suna iya kira tarurrukan wakilai domin tattauna muhimman batutuwa da tsai da kudurai kansu idan ya zama wajibi.Kwamitin dake neman kira taron wakilai ke da ikon tsai da adadin mahalartan taron da hanyar da ake bi wajen samun wakilai mahalartan.Kafa wata sabuwar kungiyar jam'iyyar ko a soke wata tsohuwar kungiyar,ya kamata a sami izni daga sassan sama na jam'iyyar.Kwamitin tsakiya na jam'iyyar da kwamitocinta na yankuna suna iya kafa wata hukumar dake wakiltarsu.

A duk lokacin da ba a yi taron wakilai na jam'iyyar na mataki daban daban ko taron wakilai na sassa,idan kungiyar jam'iyyar ta ga abin da ya zama wajaba,ta iya tura wani mutum da ya zama mai azzimar kungiyar sassan kasa ko ta nada wani mutum daban da ya zama mai azzimar kungiyar sassan kasa.Yayin da hukumar shugabanci ta jam'iyyar dake mataki daban daban ta tsai da kuduri kan muhimman batutuwan da suka shafi sassan kasa,a galibi dai ta sami ra'ayoyi daga kungiyoyin jam'iyyar dake sassan kasa.Dukkan batutuwan da kungiyoyin jam'iyya na sassan kasa ke da ikon daidaita su,bai kamata kungiyoyin jam'iyya na sassan sama su sa hannu a ciki ba in babu wani abu na musamman da ya faru.

Duk muhimman manufoffi da suka shafi duk kasa baki daya,sai kwamitin tsakiya na Jam'iyyar kadai ke da ikon tsai da kuduri,kungiyoyin jam'iyyar na ma'aikatu da na yankuna suna iya bayar da nasu shawarwari,ba su iya tsai da kudurai ko bayar da ra'ayoyinsu ga ketare su da kansu ba.Ya kamata dukkan kungiyoyin jam'iyyar na sassan kasa su tsaya haikan su aiwatar da kudurin kungiyoyi na samansu.Idan kungiyoyin jam'iyyar na sassan kasa su ga kudurin na sassan samansu bai dace ainihin halin da ake ciki a yankunansu ko ma'aikatunsu,suna iya neman a gyara.Idan kungiyar dake sama ta nace ga kudurin da ta tsaida a da,ya kamata kungiyar dake kasa ta aiwatar da shi,bai kamata ta bayar da ra'ayinta daban a fili ba,tana da ikon bayar da rahoto kan batun ga sassan dake sama sama.Ya kamata jaridu da mujjaloli da sauran kafofin yada labarai na kungiyoyin jam'iyyar dake mataki daban daban su wayar da kan jama'a kan tafarko,ka'idoji,manufoffi da kudurai na jam'iyyar.Duk lokacin da kungiyar jam'iyyar ke tattauna batutuwa,ya kamata a bi ka'idar tsiraru na bi rinjaye.

Yayin da ake tsai da kuduri kan muhimman batutuwa,sai a tsai da shi ta hanyar kada kuri'a.Ya kamata a yi la'akari da ra'ayoyi na tsiraru idan ra'ayinsa ya sha bamban da na saura.Idan an samu gardama kan muhimman batutuwa,kuma mutanen da ke ra'ayoyi daban kusan daya ne,ya kamata a tsai da kuduri bisa ra'ayin mutane da suka fi yawa,ko ba a tsai da kuduri nan da nan ba ba tare da la'akari wani hali na musamman ba.Idan aka cikin wani hali na musamman,sai a ba da rahoton kan batun ga kungiyar sama da neman kudurinta.Idan wani dan kwaminis ya ba da muhimmin ra'ayi a madadin kungiyar jam'iyya a haraba da ta wuce da'irar da kungiyar jam'iyyar ta kayyade masa,ya kamata a mika rahoto kan batun nan zuwa ga kungiyar jam'iyyar dake samansa ko a nemi ra'ayi daga kungiyoyin sama na jam'iyyar,kowane dan kwaminis ko shi babba da karami,ba shi da ikon tsai da kuduri kan muhimman batutuwa.Idan wani muhimmin hali ya zo,da ya kamata shi kansa ya tsai da kuduri,sai ya ba da rahoto cikin gaggawa ga kungiyar jam'iyyar bayan da ya daidaita batun.

Lokacin shirinmu kayadadde ne.shi ya sa ba mu da isashen lokaci na bayyana abin da kuke bukata game da Jam'iyyar Kwaminis ta Sin wadda ita ce daya take wajen tafiyar da harkokin mulki a kasar Sin.To,yau mu kwana nan sai wani lokaci mai zuwa.(Ali)