Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-09 16:10:18    
Tarihin filin wasan kwallon kafa na Santiago Bernabeu

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Mohammed Nuhun, wanda ya fito ne daga birnin Kano da ke tarayyar Nijeriya. A cikin wata wasikar da ya turo mana, ya ce, ina so a ba ni cikakken tarihin shahararren filin wasan kwallon kafan nan na Santiago Bernabeu, wacce take a kasar Spain. To, jama'a masu sauraro, don amsa tambayar, a cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku takaitaccen bayani kan wannan shahararren filin wasan kwallon kafa.

Masu sauraro, bisa gasar da aka shirya tsakanin kungiyar wasan kwallon kafa ta Real Madrid da ta Os Belenenses a ran 14 ga watan Disamba na shekarar 1947, a hukunce ne aka kaddamar da filin wasan kwallon kafa na Santiago Bernabeu, wanda ke birnin Madrid, babban birnin kasar Spain, wanda a lokacin ya kasance filin wasa mafi kyau kuma mafi zama na zamani a duniya. Daga baya, sakamakon fadada shi da aka yi a shekarar 1954, ya kuma zamanto filin wasan da ya fi girma.

A nan wurin, akwai wani mutumin da bai kamata a manta da shi ba, wato shi ne Santiago Bernabeu, wanda ya shugabanci wannan kasaitaccen aiki cikin nasara sakamakon imaninsa da kuma hangen nesa da ya yi, har ma ana kiran wannan filin wasan da sunansa. Sabo da kokarinsa, ya cimma burinsa na gina wani babban filin wasan da ke iya daukar dimbin masu sha'awar kungiyar wasan kwallon kafa ta Real Madrid.

Kafin a gina filin wasan nan na Santiago Bernabeu, kungiyar Real Madrid ta taba gudanar da gasanninta a filayen wasan kwallon kafa manya da kanana iri daban daban, ciki har da shahararren filin wasan kwallon kafa na Hipodromo. Daga baya, a shekarar 1912, kungiyar ta kaura zuwa filin wasa na O'Donnell. Sa'an nan, bayan shekaru 11, kungiyar ta sake kaura har zuwa filin wasan Ciuda Lineal, wanda ke iya daukar masu sha'awar wasan kwallon kafa 8,000. Daga bisani, a shekarar 1924, kungiyar ta kaura zuwa wani sabon filin wasa, wato filin wasa na Chamartin, wanda ya kasance filin wasa na farko da ke karkashin mallakar kungiyar. Wannan filin wasan kwallon kafa na Chamartin yana iya daukar masu sha'awar wasan kwallon kafa har dubu 22 da 500.

Amma bayan da Mr. Santiago Bernabeu ya hau kan kujerar shugabancin kungiyar a shekarar 1943, yana ganin wannan filin wasa bai dace da kungiyar Real Madrid ba wadda ke neman zama kungiyar wasan kwallon kafa mafi girma a duniya. Sabo da haka, a shekarar 1944, an fara gina wani sabon filin wasa, wanda da ma ke da sunan "La Castellana", kuma a shekarar 1955, an canza sunansa zuwa "Santiago Bernabeu ". Filin wasan Santiago Bernabeu na iya daukar mutane har dubu 75 da 432.

Sai kuma ya zuwa farkon shekarar 1980, a karo na farko ne aka yi wa filin wasan babbar gyara, ta yadda filin wasan zai iya samun iznin gudanar da gasar cin kofin duniya. Bisa gyarar da aka yi, an gyara shigar filin wasan da kuma hanyoyinsa da su zama na zamani, kuma yawan mutanen da yake iya dauka ma ya karu har zuwa dubu 90.(Lubabatu)