Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-09 15:48:30    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (02/05-08/05)

cri

Kwanakin baya ba da dadewa ba,hukumar da abin ya shafa ta sanar da cewa,za a kammala aikin gina filin gasar wasan tseren doki na taron wasannin Olimpic na Beijing na shekarar 2008 a Hongkong,yankin musamman na kasar Sin a watan Yuni na bana.A watan Yuli na shekarar 2005,a gun cikakken taro na karo na 117 na kwamitin wasannin Olimpic na kasashen duniya da aka yi a kasar Singapore,bangarori daban daban sun tsai da cewa za a yi gasar wasan tseren doki ta taron wasannin Olimpic na Beijing a Hongkong.

Ran 6 ga wata,a gun budaddiyar gasar wasan kwallon badminton ta Singapore,`yan wasan kasar Sin sun zama zakaru uku daga cikin zakaru biyar,wato `yan wasa Cai Yun da Fu Haifeng sun zama zakaru na gasar dake tsakanin maza biyu biyu,`yan wasa Zhang Yawen da Wei Yili sun zama zakaru na gasar dake tsakanin mata biyu biyu,banda wannan kuma,`dan wasa Chen Yu ya samu lambatu na gasar wasan na maza,`dan wasa daga Thailand ya zama zakara na maza.

Ran 6 ga wata,aka kammala gasar tsinduma cikin ruwa ta tashar Canada ta gasar ba da babbar kyauta da hadaddiyar kungiyar wasan iyo ta duniya ta shirya a birnin Montreal na kasar,kungiyar `yan wasan tsinduma cikin ruwa ta kasar Sin ta samu zakaru 3,gaba daya ta samu zakaru biyar a wannan tasha,yawan lambobin zinariya da ta samu ya zama lambawan.

Ran 5 ga wata,a gun gasar ba da babbar kyauta ta shekarar 2007 da kungiyar wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya ta shirya a birnin Osaka na kasar Japan,`dan wasa daga kasar Sin wanda ya taba zama zakaran taron wasannin Olimpic Liu Xiang ya zama zakaran wasan gudun tsallake shinge na mita 110 da dakika 13 da 14,Liu Xiang yana fatan zai samu sabon ci gaba a gun gasar cin kofin duniya da za a yi a watan Agusta na bana.Wani `dan wasan kasar Sin daban Shi Dongpeng ya zama lambatu na wasan.(Jamila zhou)