Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-09 15:47:03    
Wani bikin yanayin sararin samaniya na kasar Sin, wato ranar bikin Guyu

cri

Bukukuwan yanayin sararin samaniya na kasar Sin suna da tarihin da yawan shekarunsu ya kai dubu biyu ko fiye. Su ne abubuwan tarihi na al'adu da mutanen zamanin aru-aru na kasar Sin suka samu bayan da suka dudduba da nazari da kuma takaita abubuwa kan yanayin sararin samaniya cikin 'yanci kuma cikin dogon lokaci. Suna iya bayyana sauye-sauyen yanayin sararin samaniya da ruwan sama da sauran sauye-sauyen da ake samu bisa yanayin sararin samaniya da kuma ba da jagoranci ga ayyukan noma, sun ba da tasiri sosai ga abinci da sutura da tafiye-tafiye da sauransu na dubban iyalai. A takaice dai, an kasa shekara daya cikin matakan lokaci 24 bisa yanayin sararin samaniyia, a kowane matakin,alamar yanayin sararin samaniya ba ta sauya sosai ba, kuma an dora matakin da wani suna. A kowane wata, ana iya samun bukukuwan yanayin sararin samaniya guda biyu. Alal misali, a watan Afril, a farkon rabin watan, an sami ranar bikin Qingming, amma a karshen rabin watan, an sami bikin Guyu. Bikin Guyu na shekarar da muke ciki ya zo ne a ranar 20 ga watan .

Ana kan bayyana bikin Guyu cewa, daruruwan hatsi suna kamawa cikin ruwan sama. Abin da ake nufi a nan shi ne , ana iya samun isasshen ruwan sama a lokacin nan, kuma ana ruwan sama a lokacin dacewa , shuke-shuken gona suna shanyen ruwan sama suna kamawa sosai, kuma suna girma sosai. Saboda haka, a zamanin aru-aru a kasar Sin , an sami karin magana cewa, a ranar bikin Qingming, ya kamata a dasa bishiyoyi da yawa, amma a ranar bikin Guyu, ya kamata a mai da hankali ga ayyukan noma, wato shuka ire-iren amfanin gona ke nan, kafin bikin Guyu ko bayansa, ya kamata a dasa kabewa da gujiya tare da sauran irinsu da kuma shuka wake, abin da ake nufi a nan shi ne abin da yake da nasaba da huldar da ke tsakanin ruwan sama da ayyukan noma.

Lokacin bikin Guyu ya zo, zafin yanayin sararin samaniya ya fi samun sauye-sauye da yawa a cikin shekara daya, wani lokaci, ana yin zafi sosai, wani lokaci daban, ana ruwan sama da yawa bisa sanadiyar samun iskar sanyi daga arewancin kasar Sin, wani lokacin ma ana yin kankara mai karfi da samun sauran bala'in yanayin sararin samaniya, wannan yana kawo cikas ga ayyukan noma. A ranar bikin Guyu, in an sami ruwan sama da yawa, ko ma an sami bala'in fari mai tsanani, to tabbas ne za a samu mummunan tasiri ga yawan amfanin gona da za a samu. Mutanen zamanin aru-aru na kasar Sin sun tattara fasahohin da aka samu daga ayyukan noma a cikin dubban shekaru, sa'anan kuma sun sami hanyoyin da suka bi don maganin sauye-sauyen sararin samaniya da yawa da kuma kama lokacin da ke dacewar ayyukan noma sosai. Alal misali,bayan ranar bikin Guyu, wasu mutane su kan je aiki maza maza don shuka dankali mai zaki a wasu wurare masu karancin ruwan sama, ta hakan, in yanayin zafi ya zo, to dankali mai zaki yana girma da kyau sosai, wato za a iya samunsu da yawa.

Kowa ya sani, kasar Sin ta yi suna sosai a duniya wajen fitar da ti . Al'adun ti yana daya daga cikin muhimman abubuwan al'adun gargajiyar kasar Sin. A cikin al'adun ti na kasar Sin, ana son shan sabon shayi da aka samu, alal misali, ana fi son shan sabon koren shayi da aka samu a shekarar da ake ciki, amma abu mafi kyau gare mu ba sabon koren shayi da aka samu tun lokacin wurwuri ba, wannan yana da nasaba da yanayin sararin samaniya, sabon koren shayin da aka cire daga bishiyoyin shayi kafin ranar bikin Qingming, , launin shayin shi ne kore shar sosai, kamshinsa nada kamshin yanayin bazara, irin wannan shayin an mayar da shi bisa matsayin koli . Amma bayan ranar bikin Qingming zuwa ranar kafin bikin Guyu, ganyayen da aka cire kuma aka maido su don su zama shayi, mutane sun fi son shan su, kodayake shayin yana da dan daci, amma yana da daraja sosai.(Halima)