Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-08 19:30:59    
Tabkin Erhai

cri

Salamu alaikum. Jama'a masu sauraro. Barkanku da war haka. A wannan mako ma za mu kawo muku shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin wanda mu kan gabatar muku a ko wace ranar Talata. A cikin shirinmu na yau, kamar yadda mu kan saba yi, da farko za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan tabkin Erhai da ke lardin Yunnan, daga bisani kuma za mu karanta muku wani bayanin da ke cewa, gidan ibada na Xuankongsi, wato wani ginin da aka gina a sararin sama.(music)

Takbin Erhai mai fadin misalin murabba'in kilomita 250 yana a gabashin gindin tsaunukan Cangshan, ya yi suna ne a matsayin takin bakin ruwa. Tsayinsa ya kai misalin kilomita 40 daga arewa zuwa kudu, misalin kilomita 7 zuwa 8 daga gabas zuwa yamma, yana kasancewa a kan wani tuddu mai tsayin mita 1980 daga leburin teku. Siffar tabkin Erhai ta yi kama da hilali. Don nuna babban yabo ga kyawawan wurare masu ni'ima a kewayen tabkin Erhai, mutane su kan ce, ana iya ganin sararin samaniya a cikin wannan tabki sai kai ce wani babban madubi, sa'an nan kuma, tsaunukan da ke kewayen tabkin Erhai suna kasancewa tsanwa shar a duk shekara. Kifaye iri daban daban da yawa suna zama a cikin wanann tebki. Saboda siffarsa ta yi kama da wani kunnen mutum, wato Er ko kuma Erduo a Sinance, kuma igiyar ruwa na da karfi a nan, wadda ta yi kama da yadda ake cikin teku, wato Hai a bakin Sinawa, shi ya sa ake kiransa tabkin Erhai.

An gina wani wurin shakatawa a kudancin gabar tabkin Erhai, wanda nisan da ke tsakaninsa da birnin Xiaguan ya kai misalin kilomita 2. Bisa abubuwan da ke cikin littafi mai suna Man Shu, wato wani littafin tarihi da magabata suka rubuta game da Yunnan, an ce, sarakunan zamanin daular Nanzhao sun taba kiwon bareyi don yin fatauci, kuma an taba kiran wurin da sunan 'babban dutsen Xilongshan' a zamanin daular Tang. Yanzu wurin shakatawa na Erhai na karbar mutane daga wurare daban daban, inda aka dasa itatuwa da furanni da sauran tsire-tsire da yawa. An kuma fito da gine-gine ta hanyar gargajiya ta kasar Sin a nan.

Saboda wurin da wannan wurin shakatawa ke ciki, shi ya sa masu yawon shakatawa suke samu taimako wajen kallon tsaunukan Cangshan da kuma tabkin Erhai daga wurin shakatawa na Erhai.

To, jama'a masu sauraro, karin bayanin da muka yi game da tabkin Erhai na lardin Yunnan da kuma wani wurin shakatawa da ke kusa da shi ke nan. Bayan da kuka dan huta kadan, bari mu ci gaba da shirinmu na yau, za mu karanta muku wani bayanin musamman, mai suna kai ziyara ga gidan ibada na Xuankongsi, wato wani ginin da aka gina a sararin sama. Masu yawon shakatawa su kan ji mamaki sosai a lokacin da suke kai ziyara ga wannan gini mai ban mamaki.