Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-08 19:09:38    
Jarirai za su samu cikakkiyar basira idan iyayensu mata sun kara cin kifayen teku

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku wani bayani kan cewa, jarirai za su iya samun cikakkiyar basira idan iyayensu mata masu ciki suna yawan cin kifayen teku, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan wata kungiyar yin mu'amala tsakanin matasa wajen ba da ilmin jima'i ta kasar Sin. To, yanzu ga bayanin.

Bisa sakamakon nazarin da manazarta na kasar Amurka suka yi a 'yan kwanakin nan da suka gabata, an ce, idan mata suna yawan cin kifayen teku da kuma sauran abincin teku lokacin da suke da ciki, to jariransu za su fi samun basira idan an kwatanta su da sauran jarirai.

Manazarta na cibiyar nazari kan kiwon lafiya ta kasar Amurka sun ba da rahoto a kan mujallar The Lancet ta kasar Birtaniya, cewa sun gudanar da wani bincike cikin dogon lokaci ga yaran mata 'yan kasar Birtaniya da yawansu ya kai kusan 9000, kuma nufinsu shi ne su san wane irin tasiri ne cin abincin teku ga mata masu ciki zai bai wa yaransu.

Daga baya kuma manazarta sun gano cewa, idan matsakaicin yawan abincin tekun da mata masu ciki suka ci a ko wane mako ya kai fiye da giram 340, to yaransu za su fi kyau a fannin basira da lafiyar jiki idan an kwantanta su da sauran yara. Haka kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, kwarewar yara wajen motsa jiki da yin mu'amala da sauran mutane ta fi kyau lokacin da suke jarirai idan iyayensu mata sun ci abincin teku da yawa lokacin da suke da ciki. Kuma wadannan yara sun nuna gwaninta sosai wajen daidaita aikace-aikacensu lokacin da shekarunsu ya kai 7 da haihuwa, haka kuma kwarewarsu wajen magana tana da matukar kyau lokacin da shekarunsu ya kai 8 da haihuwa. Amma game da yaran da iyayensu mata ba su ci abincin teku ko kadan ba lokacin da suke da ciki, kusan kashi 50 bisa dari daga cikinsu kwarewarsu wajen magana ba ta da kyau idan an kwatanta da yaran da iyayensu mata su kan ci abincin teku lokacin da suke da ciki.

Mr. Joseph wanda ya kula da binciken yana ganin cewa, yara suna da kyau sosai idan iyayensu mata sun ci abincin teku da yawansu ya zarce giram 340 a ko wane mako lokacin da suke da ciki. Ban da wannan kuma ya bayyana cewa, abincin teku cike yake da wani irin sinadarin Fatty Acid wanda a ke kiransa OMEGA-3, wanda zai sa kaimi ga girman kwakwalwar jarirai kafin a haife su.

Amma a watan Oktoba na shekarar da ta gabata, mujallar Sabbin masu ilmin kimiyya ta kasar Birtaniya ta ba da labarin cewa, sabo da gurbatar ruwa, yawan sinadarin hydrargyrum da ke cikin kifi ya samu karuwa sosai, shi ya sa idan an ci irin wannan kifi, to zai iya yin illa sosai ga jijiyoyin jarirai kafin a haife su. Sabo da haka kwararru a kan wannan harka sun ba da shawara ga matan da suke son haifar yara da su sha magungunan ba da kariya ga lafiya da ke kunshe da man kifi domin maye gurbin danyun kifayen teku.

Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan wata kungiyar yin mu'amala tsakanin matasa wajen ba da ilmin jima'i ta kasar Sin.