Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-08 18:35:36    
Sin za ta kara karfin yaki da al'amuran ba da rashawa cikin harkokin kasuwanci

cri

Jama'a masu sauraro, assalamu alaikum, barka da war haka, barkanmu kuma da saduwa da ku a wani sabon shirinmu na "mu leka kasar Sin", kuma ni ce Lubabatu ke gabatar muku da wannan shiri daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin.

Masu sauraro, kwanan baya, mataimakin sakataren kwamitin ladabtarwa na tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, malam He Yong ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, Sin za ta kara karfin kulawa da al'amuran ba da rashawa cikin harkokin kasuwanci, ta yadda za a kara sa kaimi ga tattalin arziki da zaman al'umma da su bunkasa cikin sauri kuma yadda ya kamata.

A shekarar 1996, gwamnatin kasar Sin ta taba bayar da ka'idojin wucin gadi kan hana ba da rashawa cikin harkokin kasuwanci, inda aka tsara cewa, ba da rashawa cikin harkokin kasuwanci na nufin, 'yan kasuwa su ba da kudade ko sauransu domin sayar da kayayyakinsu ko kuma sayen kayayyaki. Bisa bunkasuwar tattalin arzikin kasuwanci, illolin da ake sha sakamakon ba da rashawa cikin kasuwanci suna ta kara daukar hankulan al'ummar kasar Sin, kuma yaki da ba da rashawa cikin harkokin kasuwanci shi ma ya zama wani babban nauyin da ke bisa wuyan gwamnatin kasar Sin a fannin yaki da cin hanci da rashawa.

A halin yanzu dai, jami'an sassan da abin ya shafa na larduna da birane da jihohi masu zaman kansu 31 na kasar Sin da kuma jami'an da abin ya shafa na gwamnatin tsakiyar kasar suna nan birnin Beijing don yin shawarwari kan yadda za a yaki da ba da rashawa cikin harkokin kasuwanci. Yayin da aka tabo magana a kan muhimmancin sa kaimi ga aikin yaki da ba da rashawa cikin harkokin kasuwanci, malam He Yong, mataimakin sakataren kwamitin ladabtarwa na tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin, ya ce,"sa kaimi ga aikin yaki da karbar rashawa cikin harkokin kasuwanci yana da muhimmancin gaske wajen kyautata muhallin zuba jari na kasar Sin da kuma kara karfin jawowa jarin waje, haka kuma yana da muhimmanci ga kamfanonin kasar Sin masu karfi da amana da su shiga duniya don yin takara."

Gine-gine da sayar da filaye da cinikin 'yancin mallaka da sayayyan da gwamnati ke yi da cinikin magungunan sha da bunkasa albarkatun kasa da kuma sayar da su sun kasance fannonin da a kan samu ayyukan ba da rashawa. A cikin 'yan shekaru biyu da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta gudanar da aikin yaki da karbar rashawa cikin harkokin kasuwanci musamman a cikin wadannan manyan fannoni shida da kuma sauran fannoni 9, wato su ne ba da rancen kudi da bankuna ke yi da sayar da takardun shaidar kudi bisa farashin gaba da ba da inshorar kasuwanci da wallafe-wallafe da wasan motsa jiki da sadarwa da bunkasa wutar lantarki da binciken ingancin kayayyaki da kuma kiyaye muhalli. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, daga watan Agusta na shekarar 2005 har zuwa watan Maris na shekarar 2007, gaba daya ne kasar Sin ta daidaita al'amuran da suka jibinci rashawa cikin harkokin kasuwanci da yawansu ya wuce dubu 21.

Ko da yake gwamnatin kasar Sin ta sami manyan nasarori wajen yaki da ba da rashawa cikin harkokin kasuwanci, amma duk da haka, ana ci gaba da fuskantar matsala mai tsanani ta ba da rashawa cikin harkokin kasuwanci a wasu fannoni. A gun wannan taron shawarwari, malam He Yong ya kuma bayyana a fili cewa, matsalar yin amfani da ikonsu ba kamar yadda ya kamata ba da wasu hukumomin kasa da kuma ma'aikatansu suke yi sun zama ruwan dare. Ya kuma nemi wurare daban daban da kuma hukumomi daban daban da su dauki matakai kamar yadda ya kamata, ta yadda za a kara karfin yaki da rashawa cikin harkokin kasuwanci. Ya ce,"Ya kamata har kullum mu dora muhimmanci a kan aikin yaki da rashawa cikin harkokin kasuwanci, kuma mu kuduri aniyyar kara warware wasu manyan laifuffuka, za mu mai da hankali a kan kulawa da laifuffukan da ma'aikatan gwamnati suke yi na yin amfani da ikonsu ba kamar yadda ya kamata ba wajen neman karbar rashawa cikin harkokin kasuwanci, kuma za mu mai da hankali kan ayyukan ba da rashawa cikin harkokin kasuwanci wadanda suka lalata moriyar jama'a kwarai."