|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2007-05-08 10:31:42
|
|
A warware rikicin Darfur ta hanyar siyasa
cri
A warware rikicin Darfur ta hanyar siyasa Bisa labarin da kamfanin dillancin labarai na Hsinhua ya bayar,an ce a ran 7 ga wata jami'an kungiyar kasashen Larabawa da na Majalisar dinkin duniya da kuma kungiyar tarayyyar Afrika sun yi kira a daidaita rikicin Darfur na kasar Sudan ta hanyar siyasa kuma sun bayyana cewa wannan hanya daya tak wajen shawo kan rikicin Darfur. A wannan rana a birnin Alkahira Moussa ya gana da Jan Elisson,manzon musamman na sakatare janar na MDD kan batun Darfur da Salim Ahmed Salim,manzon musamman na kungiyar tarayyar Afrika kan batun Darfur wadanda suka kawo ziyara.Mr Moussa ya ce bangarori uku sun tattauna halin da ake ciki a yankin Darfur a halin yanzu da rawar da hukumomin nan uku ke iya takawa kan batun Darfur,sun cimma daidaito kan batun nan. Mr Salim ya yi kira a daidaita rikicin Darfur ta hanyar sulhuntarwa da kungiyar kasashen Larabawa da MDD da kuma kungiyar tarayyar Afrika ke yi da hukumomi na bangare da duniya su taka rawa a ciki. Mr Jan Eliasson ya jadadda cewa ba za a iya daidaita matsalar Darfur da karfin soja ba sai ta hanya daya tak ta siyasa.(Ali)
|
|
|