Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-07 19:11:31    
Takaitaccen bayani game da kabilar Tujia

cri

Kabilar Tujia tana daya daga cikin kananan kabilun kasar Sin. Yawancin 'yan kabilar suna da zama a yankunan tsaunin Wuling da ke hade lardin Hunan da Hubei da Sichuan da Guizhou. Bisa kididdigar da aka yi a duk fadin kasar Sin a shekara ta 2000, yawan mutanen kabilar Tujia ya kai fiye da miliyan 8 da dubu 20. Suna amfani da yarensu, amma babu harrufa. 'Yawancinsu sun iya harshen Sinanci

A da, 'yan kabilar Tujia sun yi aikin gona kawai. Amma ba su iya samun hatsi da yawa ba sakamakon koma bayan fasahar noma da kayan aikin noma. Sabo da haka, sun koyi fasahar noma da shigar kayayyakin noma daga wajen 'yan kabilar Han domin kara saurin cigaban tattalin arziki da zaman al'umma na kabilar Tujia. Kafin shekarar 1949, yankunan kabilar suna koma baya sosai sakamakon yake-yaken da aka yi. 'Yan kabilar sun sha wahalhalu sosai.

Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin a shekarar 1949, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar sun tsara da kuma aiwatar da manufofin kabilu iri daban daban a yankunan kananan kabilu ciki har da yankunan da 'yan kabilar Tujia suke da zama. Sannan kuma an kafa shiyyar Xiangxi ta kabilar Tujia mai cin gashin kanta a shekarar 1957. A shekarar 1983, an kuma kafa shiyyar Xiangxi ta kabilar Tujia da ta Miao mai cin gashin kanta. Bugu da kari kuma, an kafa gundummomin kabilar Tujia masu cin gashin kansu guda 5. A karkashin taimakawa da tallafawar gwamnati, galibin jama'ar kabilar Tujia da ke da zama a yankunan tsaunin Wuling sun riga sun kubutar da kansu daga mawuyacin hali, kuma suna kama hanyar neman arziki.

A cikin dogon tarihin da ya wuce, 'yan kabilar Tujia sun kirkiro adabi da al'adunsu iri daban-daban ciki har da tatsuniyoyi da rubutattun wakoki da kide-kide da wasannin kwaikwayo iri iri.

'Yan kabilar Tujia suna kokarin sarin gonaki da kama kifi. Abincin da suke ci yana kunshe da masara da shinkafa. Tufafin da 'yan kabilar mata suke sanya suna kama da na matan kabilar Han. Sai a gun bukukuwansu, suna sanya tufafin da ke bayyana halayen musamman da al'adun musamman na kabilar.

A da, iyaye ne suke neman aure ga 'ya'yansu. Matasa ba su da 'yancin neman soyayya. Amma yanzu, suna da 'yancin neman soyayya da aure da kansu. A waje daya, a wasu kauyuka, har yanzu iyaye ne suke neman aure ga 'ya'yansu.

Bisa al'adar kabilar Tujia, suna taya murnar bakukuwa a ran 8 ga watan Afirlu da ran 6 ga watan Yuni da sabuwar shekara ta kabilar bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. Bikin sabuwar shekara ta kabilar gaggarumin biki ne ga kabilar. (Sanusi Chen)